September 18, 2026

Zaban 2022: Aminu Ubale Ka Fito Domin Ceton Karamar Hukumar Funtua -Matasan Funtua

0

Daga Awwal Isah, Katsina

Wata ƙungiyar matasan ƙaramar hukumar Funtua ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar ɗalibai na ƙasa reshen jahar Katsina Comrade Aliyu Usman a madadin dattawan ƙaramar hukumar Funtua sun buƙaci Comrade Aminu Ubale Funtua da ya fito takarar neman kujerar shugabancin ƙaramar hukumar ta Funtua a wannan zaɓen mai zuwa

Wannan kira dai ya biyo bayan irin rawa da matasa suke takawa wajan cigaban kowane yankin musamman yanmkin Funtua inda nan Aminu Ubale ya fito kuma ya kasance dan kishin kasa da ya kamata ya amsa kiran al’umma akan wannan bukata.

Kungiyar na da fatan cewa  ta haka ne kawai ƙaramar hukumar za ta samu ci gaba da nasarorin da bata taɓa samu ba, wanda hakan ne zai taimaka mata wurin fitowa da ƙimar gwamna Aminu Bello Masari a ƙaramar hukumar Funtua.

Kwamared Aminu Ubale ya kasance mutum ne me taimakawa ƴunƙurin gwamnan jihar Katsina wajan ganin komi an dora shi a muhalinsa tare da dawo da martabar jihar Katsina da ta rasa sakamakon mulkin ‘yan kama karya.

Ƙungiyar ta bayyana Comrade Aminu Ubale Funtua a matsayin mutum mai maida hankali akan aiki, da daɗin hulɗa ga jama’a da kuma jajircewa wurin aiki da tafiyar da shugabanci na-gari.

A cewar kungiyar yana da ƙwarewa a kan abubuwan da suka shafi matasa da sanin shugabancin al’umma a wannan lokacin.

Idan za’a iya tuna Aminu Ubale shi ne mataimakin shugaban majalissar matasan Najeriya a yankin  arewacin Najeriya kuma shi ne shugaban ta na ƙaramar hukumar Funtua, wanda ya tashi cikin al’ummar yankin, kuma ya bada gudunmuwa wurin gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa, da na ‘ƴan majalisun dokoki na ƙasa da zaɓukan ‘ƴan majalisun dokoki na jiha, dama zaɓen gwamnan jihar Katsina a shekarar 2015 da 2019.

Haka kuma kungiyar na cike da sa ran cewa, Comrade Aminu zai amsa wannan babban kira da aka yi ma sa, saboda ba takarar shi bace, ta matasa da dattawan Funtua ce. Mutane sun kuma ba shi tabbacin goyan baya ɗari bisa ɗari don yin wannan aiki na ceton al’umma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *