September 18, 2026

An Naɗa Ferfesa Bichi Mamba A Hukumar Gudanarwa Ta Jami’ar Maryam Abacha, Kano

0

Hukumar gudanarwar ta jami’a Maryam Abacha de ke Kano ta naɗa mataimakin shugaban jami’ar Gwamnatin Tarayyar da ke Dutsima a jihar Katsina, (FUDMA) Ferfesa Armaya’u Hamisu Bichi a matsayin mamba na hukumar gudanarwa.

Bayanin hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar FUDMA kwamared Habibu Umar Amin ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai a Katsina.

Haka kuma sanarwa ta ce nadin Ferfesa Bichi ya zo ne bayan amincewar hukumar gudanarwa ta MAAUN bayan kammala wani taro da ta yi a ranar 25 ga febrairu , 2022 a jihar Kano.

Da yake taya Ferfesa Bichi murna shugaba kuma wanda ya asasa jami’ar Maryam Abacha, Ferfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ce zaɓan Bichi ya biyo bayan dogon nasiri kafin lalubushi cikin dubu saboda ƙima da girma da kuma yadda ya sadaukar da kansu wajan cigaban ilimi da al’umma.

“Zaɓen da aka yiwa Ferfesa Bichi ya ƙara tabbatar da nagartarsa musamman ƙoƙarin sa wanda ya zama misali akan bada tallafin karatu da sauran ɗalibai, saboda haka ina ƙara tayaka murna” inji Gwarzo

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *