September 18, 2026

Zaɓen Fidda-Gwani Na APC Ya Bar Baya Da Ƙura A Bade/Jakusko

0

Daga M. Shamsudeen, Yobe

Wasu daga cikin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki a jihar Yobe, daga ƙananan hukumomin Bade da Jakusko sun gudanar da gangamin nuna rashin jin-daɗi tare da sake yin ƙira ga uwar jam’iyyar ta ƙasa da cewa ta yi musu adalci wajen zaɓen fidda-gwani a mazaɓar Bade/Jakusko a kujerar majalisar wakilai.

Al’ummar dai sun bayyana rashin gudanar da sahihin zaɓen tamkar tauye haƙƙin al’ummar yankin ne a dimukuraɗiyance.

Waɗannan kiraye-kirayen sun fito ne daga bakin ɗan takarar kujerar majalisar wakilai, mai wakiltar Bade/Jakusko, Hon. Sani Ahmed Kaitafi tare da magoya bayan sa a wani gangamin da su suka shirya ranar Litinin a garin Gashuwa, shalkwatar ƙaramar hukumar Bade da ke jihar Yobe, inda suka nanata yin kira da buƙata ga uwar jam’iyyar cewa, kimanin kwanaki biyar da suka gabata wanda jam’iyyar APC ta fara gudanar da zaɓen fidda-gwani a faɗin Nijeriya, yayin da har yanzu ba a gudanar da na Bade/Jakusko ba.

Magoya bayan ɗan takarar sun ɗora zargin ƙin yin zaɓen ne ga kwamitin da uwar jam’iyyar ta tura a yankin, wanda hakan ya saɓa wa tanadi da ƙudirin jam’iyyar APC wanda ya ƙunshi yi wa kowane ɗan jam’iyya adalci ta hanyar gudanar da shi ko kuma sulhu tsakanin ‘yan takara domin samun haɗin kai da ci gaban jam’iyyar da al’umma baki ɗaya, inda suka kafe kan cewa, “amma babban abin mamaki, ko ɗaya bai yuwu ba; ba a yi zaɓen fidda-gwani ba balle kuma sulhunta ‘yan takarar.”

“Yau kwana biyar cur (Jummu’a zuwa Litinin) da fara gudanar da zaven, amma abin takaici an ƙi gudanar da na Bade/Jakusko, alhalin takwarorin yankin a jihar Yobe da sauran yankunan Nijeriya sun yi nasu, kuma har yanzun nan ba a gaya mana dalili ba.

Sai kawai mu ka ji labari a sama cewa wai wani ya ci zaɓen. Abin tambaya shi ne; a ina aka gudanar da zaɓen kuma a gaban wa aka yi shi? Saboda mu dai iya sanin mu ba a gayyaci xan takarar mu ba kuma ba a yi zaɓen ba inda uwar jam’iyyar APC ta ayyana.”

A wannan gangamin wanda magoya bayan Hon. Kaitafi su ka gudanar, sun yi kira ga uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta shiga lamarin tare da yi musu adalci wajen gudanar da zaɓen fidda-gwani a mazaɓar Bade/Jakusko da ke jihar Yobe, kamar yadda ta yi a sauran yankunan jihar da a kowace mazaɓa a faɗin ƙasar nan.

Ɗaruruwan magoya bayan waɗanda suka gudanar da taron gangamin a wasu titunan garin Gashuwa, kana kuma ɗauke da kwalaye da alluna an rubuta mabanbantan bayanai waɗanda suke ɗora zargi ga kwamitin da jam’iyyar APC ta ɗorawa alhakin zaɓen fidda-gwanin, bisa yadda suka ƙi gudanar dashi face kawai sun shiga zaki tare da rubuta sunan wani mutum wanda ba shi ne zaɓi al’ummar yankin ba.

Da yake jawabi ga dandazon matasan da suka gudanar da gangamin, daraktan yakin neman zaɓen Hon. Kaitafi, Mallam Bukar Dala ya bayyana cewa, “Bamu gamsu ba, saboda sam ba a gudanar da zaɓen fidda-gwani ba, kawai sai labarin muka ji cewa sun shiga ɗaki tare da rubuta sunan wani mutum a matsayin wanda aka zaɓa alhalin babu inda aka yi zaɓen- wannan wasa da hankali ne kawai suka yi.” In ji shi.

Shima Malam Bashir Rankas ya yi ƙarin hasken cewa, “Bisa gaskiyar zance shi ne; duk da na matsayinmu ya’yan jam’iyyar APC, amma ba a gudanar da zaɓen fidda-gwani na mazavar Bade/ Jakusko ba, kuma mun yi mamakin yadda hakan ya faru saboda mun ga yadda aka gudanar dashi a faɗin ƙasar nan.

Saboda haka muna kira ga uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta yi wa al’ummar wannan yanki adalci a zo domin gudanar da shi tare da bai wa jama’a dama su zaɓi ɗan takarar da suke so. Sannan mu na so manyan mu su gane dangane da irin abin da muke ƙoƙarin kaucewa faruwar sa, don gaskiya jama’a sun harzuƙa matuƙa.” In ji shi.

A nashi ɓangaren, Hon. Sani Ahmed Kaitafi, ɗan takarar kujerar majalisar wakilai a mazaɓar Bade/Jakusko, ya yi kira ga magoya bayan sa cewa kowa ya kwantar da hankalin shi, sannan ya buƙaci uwar jam’iyyar APC ta duba lamarin tare da yi wa al’ummar yankin adalci.

Ya ce, “Ta la’akari da yanayin da ake fuskanta na tunkarar babban zaɓe a Nijeriya na 2023, wanda wasu jam’iyyu kan karkata zuwa ga yan takarar da wasu jam’iyyu ke ƙoƙarin take musu haƙƙi, wanda hakan kan iya kai wasu zuwa ga canja ra’ayi wajen canja sheƙa ko kuma su rungumi ƙaddara.” Ya bayyana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *