September 18, 2026

An Yi Taron Yaki Da Safarar Bil’adama A Abuja.

0

An buƙaci ‘yan jarida da su maida hankali kan abubuwan da suka shafi safarar bil’adama don ganin an magance matsalar.

Wani jami’in dake bada horo a wurin wani taron kwana 3 Mr. Godwin Morka ya bayyana wannan bukatar a Abuja.

Kuma wasu kungiyoyi ne suka shirya taron da aka tsara akan yaki da safarar bil’adama.

Ya bayyana safarar bil’adama da cewa abu ne da ake yi kodai da amincewar mutum, ko kuma ba tare da amincewar shi ba don tilla shi cikin ayyukan wahala, karuwanci, koma sayar da shi a matsayin bawa.

Kamar yadda ya bayyana, kididdiga ta nuna cewa, akwai yan Najeriya fiye da miliyan 1 da aka yi safarar su zuwa kasashen Mali, Cotonou, Libya, Chadi dama sauran wasu kasashen nahiyar turai.

Mr. Godwin Morka ya ce daga cikin wannan adadin, akwai yan mata miliyan 50 yan Najeriya da abun ya shafa.

Saboda haka kungyoyin suka bukaci yan jarida su yi amfani da iliminsu wurin magance matsalar.

Mr. Godwin Morka wanda ya bayyana mahimmancin yan Jarida a cikin al’umma, ya bukaci su taimaka wurin yaki da matsalar.

Kuma sun ce taron nada nufin yin hadin gwiwa da hukumar yaki da safarar bil’adama, dama sauran hukumomin da abin ya shafa don ganin an magance matsalar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *