Dikko Raɗɗa Na Fuskantar Turjiya Daga Magoya Baya A Katsina
Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar APC Dakta Dikko Umar Raɗɗa na Fuskantar barazana da turjiya daga magoya baya a wani rangadi mai kama da yakin neman zaɓe da yake yi a faɗin jihar.
Dikko Raɗɗa na ɗaya daga cikin ‘yan takarar gwamnan jihar Katsina da ya samu nasara a zaben fidda gwani a cikin su tara da suka kwafsa takara daga ƙarshe ya yi nasara.
Acikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na zamani (social media) an nuna ɗan takarar a ƙaramar hukumar Kurfi a lokacin da yake ganawa da masu da tsaki na jam’iyyar APC inda yake cewa Najeriya mutane na amsawa da sai Atiku
Haka kuma ya riƙa cewa ƙaramar hukumar Kurfi a majalisar jiha, jama’a na amsawa da sai Shagali, shi kuma Shu’aibu Shagali ya nemi takarar majalisar dokokin jihar a jam’iyar APC bai samu nasara ba ya koma mai kayan marmari NNPP
Sai dai kuma jama’a sun amsa masa yadda yake so a lokacin da ya ke cewa jihar Katsina suka ce sai Gwagware,(Wato Shi Dikko Raɗɗa) ya ƙara da cewa Sanatan Katsina ta tsakiya suka ce sai Abdu Soja, ya ƙara faɗin Dutsima Kurfi suka ce sai ɗan arewa.
Tuni dai jama’a suka fara tofa albarkacin bakinsu game da wannan rangadi na Dikko wanda jam’iyyar NNPP ta zarge shi da cewa yaƙin neman zaɓe ne ya fara, inda ya ce a’ a gaisawa ce yake da mutanensa na arziki.
Yanzu haka za a yi yaƙin neman zaɓe yana cewa Najeriya ana amsa masa da sai Atiku yana cewa Kurfi ana cewa sai Shagali? Amsar waɗanda tambayoyi sai an zo ya’ki neman zaɓe a hukumance.
