September 17, 2026

Bai kamata a Rinƙa Yi Wa ‘Yan Fim Kallon ‘Yan Iska Ba. Cewar Hafsat Hassan

0

Daga MUKHTAR YAKUBU.

Sabuwar jaruma a Masana’antar finafinai ta kannywood Hafsat Hassan wadda aka fi sani da Amme ta yi kira ga masu kallon finafinai da su rinƙa yi musu adalci a wajen yi musu hukunci a tsakanin su da sauran Jama’a.

Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar da muka yi da ita a matsayin ta na sabuwar jaruma in da take cewa “Kada mutane su ga muna yin fim su rinƙa ɗaukar mu ‘yan Iska ne karuwai, sam wannan abin bai dace ba.

Haka kuma jarumar ta ƙara da cewa saboda haka a daina yi masu irin wannan kalaman, domin kowanne aiki ka gani, akwai nagari akwai na banza, don haka ba su taru mun zama ɗaya ba, kowa da irin yanayin da yake gudanar da rayuwar sa.

“Don kuwa babu yadda za a yi mutane su taru suna sana’a Kuma a ce duk taron su babu mutumin kirki duk na banza ne, domin kowa ya sani mu Musulmi ne don haka ba zai yiwa a cikin mu a ce babu nagari ba duk mutanen banza ne” inji ta

Ta ce idan aka yi haka ba a yi masu adalci ba. Kuma su ma masu faɗar ba su yi wa kan su adalci ba, domin mu ‘ya’yan su ne, kannen su ne “

Daga ƙarshe ta yi fatan yadda ta shigo harkar lafiya, Allah ya sa ta gama da harkar lafiya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *