September 17, 2026

Zargin Ɓata Suna: Bala Abu Ya Shigar Da Sabuwar Ƙara

0

Shari’ar zargin ɓata suna wadda Alhaji Bala Abu Musawa, ya shigar a kan Mamuda Lawal Musawa, ta dauki wani sabon Salo, sakamakon rashin samun sulhu a tsakani.

A ranar 18 ga watan Yuli, 2022, Lauya Bala Abu Alsulh Antoni, ya rubuta wata takarda zuwa ga Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina a madadin Bala Abu yana ƙarar Mamuda Lawal da ɓata masa suna.

Takardun masu shafuka biyu, wadda jaridun Katsina City News suka gani, Lauyan ya nemi, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina ya yi binciken lamarin ɓata masa suna, tare da bi masa haƙƙinsa.

Kafin wannan shigar da ƙarar ta biyu, an yi ƙoƙarin sulhu da kuma janye duk wata ƙara.

Bala Abu mai ƙara, ya kafa sharaɗin cewa, zai janye, amma sai in Mamuda ya rubuta takardar ban hakuri da karyata kansa da kansa a kan zargin da ya yi wa Bala Abu na ɓata masa suna.

Dukkanin masu shiga tsakani, har da gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, sun amince da wannan sharaɗin na Bala Abu.

Amma har zuwa 17 ga watan Yuli, Mamuda bai rubuta wannan takara ta janye kalamansa da ba da hakuri ba.

A ranar 18 ga watan Yuli, Lauyan Bala Abu ya shigar da sabuwar ƙara a ofishin Kwamishinan ‘yan sanda, yana neman su bincika lamarin, kuma su bi masa hakkinsa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *