September 17, 2026

Shugaban Karamar Hukumar Kurfi Ya Shawarci Iyaye Su Taimakawa Kokarin Gwamnati Wurin Yaƙi Da Cututtuka.

0

Karamar hukumar Kurfi ta shawarci iyaye su taimaka ma kokarin gwamnati wurin raba yara da cututtuka masu hallaka su.

Shugaban karamar hukumar Mannir Shehu ya fadi hakan a lokacin kaddamar da shirin yaki da cutar masassara a cibiyar kiwon lafiya ta Rawayau.

Shugaban karamar hukumar ya kuma bukaci matasan da suka cika shekaru 18 da haihuwa da cewa su je su yi rijistar katin zabe na dindindin.

Haka kuma ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da yin addu’a don ganin an samu zaman lafiya a jihar Katsina dama kasa baki daya.

Mannir Shehu ya kara da cewa karamar hukumar ta gyara motar sintiri ta yan sanda don inganta ayyukansu a yankin.

A jawabin shi, daraktan lafiya na karamar hukumar ta Kurfi Samisu Mani Mashi ya ce an yi dukkan tsare tsaren da suka wajaba don samun nasarar shirin, Popular News Hausa.

Maradin Katsina hakimin Kurfi Amadu Kurfi, wanda ya samu wakilcin Aliyu Rabi’u ya yaba ma gwamnatin jihar Katsina dama su kansu kungiyoyin bada tallafin bisa gudanar da shirin na yaki da cutar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *