An Fara Allurar Masassara A Jihar Katsina.
An fara gudanar allurar yaƙi da zazzabin masassara da aka saba yi duk irin wannan lokacin a karamar hukumar Bakori, Dandume, Funtua da kuma Danja.
Shirin da gwamnatin jihar Katsina hadin gwiwa da ƙungiyoyin bada agaji suka dauki dauyin shi, nada nufin yaki da cutar masassara a fadin jihar Katsina.
A karamar hukumar Bakori, shugaban karamar hukumar Ali Maicitta ne da daraktan lafiyar karamar hukumar Mansir Garba suka duba shirin.
Kuma wuraren da aka duban sun hada da Ƙofar Fada, Bakin Kasuwa, Karin Kudu da kuma Unguwar Tofa.
Ya bayyana gamsuwa da nasarar da aka samu an yankin.
Da daraktan lafiyar karamar hukumar Mansir Garba ke jawabi, ya ce an kai isassun magunguna a wurin.
A Funtua, Dandume da kuma Danja, daraktocin lafiyar kananan hukumomin sun ce shirin ya yi yadda ake so.
Garba Sule Masari, Aisha Isyaku da kuma Danjuma sun bukaci iyaye su goya ma shirin baya don cimma abinda aka sanya gaba.
