Ba Mu Sanya Jarrabawa Ranar Sallah Ba – NECO.
Hukumar shirya jarabawar kammala makarantar sikandiri ta kasa NECO ta ce ba ta sanya Jarabawa a ranar Asabar 9 ga Yuli na shekarar 2022 ba, wadda ke zama ranar Sallah.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar NECO, Azeez Sani ya bayyana cewa hakan ya sabawa rade-radin da wasu ke yi na cewa hukumar ta sanya jarabawar ranar 9 ga watan Yuli duk da cewa ranar hutun Sallah ce.
Hukumar NECO ta ce tana sane da muhimmancin bukukuwan addini, inda ta yi nuni da cewa hukumar ta kan samar da isassun tanadin irin wadannan lokuta a lokacin kayyade ranakun jarrabawa, inji majiyar Popular News Hausa ta AIT.
Ta ba da tabbacin cewa, ta bada hutun sati daya, wanda zai fara daga ranar Juma’a 8 ga Yuli zuwa Laraba 13 ga Yulin shekarar 2022 a jarrabawar kammala makarantar sakandare da ake yi wato SSCE don baiwa Musulmi samun isasshen lokacin yin bikin sallah.
Idan dai za a iya tunawa, jarrabawar kammala makarantar sakandare ta shekarar 2022 ta fara ne a ranar 27 ga Yuni, kuma ana sa ran za ta ƙare a ranar 12 ga Agusta, 2022.
