September 17, 2026

Asibitocin Katsina Na Cikin Halin Ni ‘Ya Su, An Rufe 70 Saboda Ayyukan ‘Yan Bindiga

0

Muna da tsari na gyara da ɗaukaka darajar asibitoci a jihar Katsina -Dakta Shamsudden Yahaya.

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Ƙananan asibitoci a jihar Katsina na cikin ni ‘ya su sakamakon lalacewa da rashin gyara da kuma uwa uba rashin isasun ma’aikatan lafiya da za su kula da marasa lafiya.

Ziyarar gani da ido da wakilan kafafen yaɗa labarai suka kai a wasu ƙananan asibitoci ya tabbatar da zargin da ake na lalacewa wasu daga cikin ƙananan asibitoci musamman a ƙaramar hukumar Mani ta jihar Katsina.

Wannan yanayi yana zuwa a daidai lokacin da gwamnatin jihar Katsina ke cika shekaru bakwai akan mulki wanda ana iya cewa tana gab da fara bankwana sannan a baya sun faɗa cewa sun kashe makudan kuɗaɗe a wannan ɓangare na kiwon lafiya.

Gawon Mala/ Filin KwalloJani/Shaiskawa

Asibitin Gawon Mala da ke cikin ƙaramar hukumar Mani na fuskantar rugujewa baki ɗaya saboda a iya cewa komi ya lalace a wannan cibiyar kula da marasa lafiya, yanayin da wannan asibiti take ciki bai yi daidai da kawo ɗan adam domin yi masa magani ba.

Ma’aikatan lafiya biyar ke akwai biyu na dindindin uku na wucin gadi, kuma ana buɗe asibitin sau biyu kacal acikin sati wato ranakun talata da Laraba inji masu zuwa neman lafiya.

Bincike ya tabbatar da cewa duk wanda wata rashin lafiya mai tsanani ta same shi a wannan yanki to baya da zaɓin da ya wuce zuwa asibitin tsagero da ke da nisan kilo mita goma domin neman lafiya da kuma tsira da ransa.

Haka suma jama’ar da ke wajan da suka zo kawo marasa lafiya sun kuka ai’nun akan irin halin da aka bar wannan asibiti, sannan sun yi kira ga gwamnati da ta yi wani abu domin a rage asarar rayuka.

Labarin dai iri ɗaya ne da ƙaramar asibitin da ke filin kwallo Jani domin kuwa suna fuskantar matsalolin iri guda, kuma har yanzu hukumomi ba su ce wani abu game da wannan matsala ba, kamar yadda masu zuwa neman lafiya suka tabbatar.

A garin Shaiskawa da ke kan hanyar zuwa doro kuwa lamari ya ɓaci matuƙa domin su tuni aka rufe asibitin fiye da shekaru biyu kuma koda ma’aikatan lafiyar su zo garin ranar juma’a ana basu aron wata islamiyya ne domin gudanar da aikin su.

Malam Awwal Salisu ya shaidawa manema labarai cewa haka kawai suka daina ganin ma’aikatan lafiya suna zuwa domin yin aikin su asibitin Shaiskawa daga baya kuma iska ya ɗauke rufin yanzu haka asibitin na neman komawa kofai, a ya yin da marasa lafiya sai dai su tafi Mani ko kuma wani shagon sayar da magunguna a wani Kauye kusa da su.

Durɓi Takusheyi

A wannan gari akwai asibiti wanda hukumar MDGs ta gina a shekarar 2009 kuma duk abinda ake buƙata domin kula da marasa lafiya an sanya a wannan asibiti ta garin Durɓi Takusheyi.

Daga cikin abubuwan da aka ƙawata asibitin da su, sun haɗa da gadajen kwantar da marasa lafiya da ɗakin gwaji da kujeru da tebura da sauran kayayyaki.

Amma wani abin takaici da baƙin ciki shine yadda tsuntsaye da jemagu suka mamaye wannan asibiti, inda hatta marasa lafiya ba ko da mutum ɗaya, ba abinda da zaka ji sai kukan tsuntsaye da jemagu kawai.

Mazauna garin sun tabbatar da cewa ma’aikacin lafiya ɗaya ne kuma jama’ar garin ne ke biyan sa dubu takwas duk wata, sai kuma mai gadi mutum guda wanda gwamnati ke biyansa dubu uku duk wata.

Waɗannan a ƙaramar hukumar Mani kenan, kusan haka abin yake a sauran wuraren da ayyukan da gwamnatin jihar Katsina ta fars bai kai gare su da.

Shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko Dakta Shamsudden Yahaya.

Bayan kammala wannan ziyara ta gani da ido, mun tattauna da Dakta Shamsudden Yahaya domin jin ta bakin sa gane hali da muka samu wadancan asibitoci da kuma sauran da ba mu kai ga ziyarta ba.

Dakta Shamsudden ya fara yin Shinfiɗa na Irin ƙoƙari da tsare-tsaren da gwamnatin Aminu Bello Masari ta bullo da su akan harkokin kiwon lafiya a jihar Katsina tun zuwan ta akan mulki 2015.

Ya ƙara da cewa bayan sun yi doguwar tattaunawa sun fahimci irin matsalolin da asibitoci ke fuskanta, shi yasa suka fito da sabon tsarin gyara da kuma inganta waɗannan cibiyoyin shan magani a fadin jihar Katsina.

“A jihar Katsina muna da mazaɓu 361 bisa wannan tsarin ake son a tabbatar duk mazaɓa taba da asibiti guda wanda ke da ma’aikata da kayan aiki da magunguna domin amfanin jama’ar da ke wannan mazaɓa” inji shi.

Dakta Shamsudden Yahaya ya ce sun fara da asibitoci 152 ya zuwa yanzu kuma bayan sun kammala da wannan za su sake ɗaukar sauran domin a cewar sa abin da ya wa, wai mutuwa ta zo kasuwa, sannan ya ƙara da cewa hatta asibitoci da muka ziyartan ba mantawa aka yi da su ba, suma ana tafe kansu nan gaba.

Haka kuma ya faɗa da bakinsa cewa suna fuskantar matsaloli a ƙananan hukumomin da hare-haren ‘yan bindiga ya ta’azara, wanda ya ce a dalilin haka tasa sun rufe asibitoci 69 ya ƙara da cewa yan bindiga sun ƙone guda biyu kurmus a ƙaramar hukumar Batsari.

Shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko ya ƙara da cewa an sha yin garkuwa da ma’aikatansu a lokuta daban daban amma daga baya a sake su, yanzu kuma suna fuskantar ƙalubalan canje-canjen wuraren aiki musamman mata da ke aiki a wuraren da ake kai hare-hare.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *