Gwamnatin Jihar Bauchi Zata Bada Hutu Don Yin Rijistar Katin Zabe.
Gwamnan jihar Bauchi ya bayyana ranar Litinin 27 ga watan Yunin wannan shekarar ta 2022 a matsayin ranar hutu.
Hutun nada nufin ba al’ummar jihar da suka cika shekaru 18 da haihuwa a halin yanzu damar zuwa yin rijistar katin zabe, ko sauya bayanan dake saman katin ga wadanda suka canza wurin zama, ko kuma sake ga wanda nasu ya bata.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan jihar shawara akan kafafen yada labarai Mukhtar Gidado ya fitar a Bauchi.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, gwamnan ya bayyana matukar damuwa kan ƙarancin fitowar al’ummar da suka cancaci mallakar katin kada kuri’ar, inda ya umarci kwamishinonin shi, da masu ba shi shawara, da shuwagabannin hukumomi, da kuma manyan jami’an gwamnati dake rike da ofisosi da su koma mazaɓunsu don wayar da kan al’ummar da suka cika shekarun yin zabe da su mallaki katin kada kuri’a.
Hakanan kuma sanarwar ta shawarci al’ummar jihar da su tabbatar sun mallaki katin jefa kuri’ar don ganin an dama da su a babban zaben shekarar 2023 dake tafe.
