September 17, 2026

Kungiyar MOPPAN Reshen Jihar Kano Ta Kira Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Harkar Fim.

0

Daga MUKHTAR YAKUBU

Kungiyar Kwararru ta masu shirya fim ta ƙasa wato Motion Picture Practitioners Associations of Nigeria (MOPPAN) reshen jihar Kano ta gudanar da wani zama na musamman da dukkanin ɓangarori na masu gudanar da sana’o’in su a cikin masana’antar Kannywwod da suke ƙarƙashin ta da kuma waɗanda suke da alaƙar tafiyar da harkar su tare.

Taron wanda sabon shugaban kungiyar na jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya kira a ranar asabar ɗin da ta gabata kuma aka gudanar da shi a wajen taro na Ali Jita Event Center an tattauna a kan matsalolin da suke damun harkar fim da kuma hanyoyin da za a bullo domin warware su.

Sannan a zaman an yi magana a kan gudanar da zaɓuka a kungiyoyin da su ke ƙarƙashin MOPPAN ɗin kamar daraktoci Masu ɗaukar Hoto (Camara Man) Furodusa jarumai da sauran su.

Tun dai rantsar da sabon shugaban kungiyar Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya sha alwashin farfaɗo da darajar harkar fim da masu gudanar da ita, da kuma samar da hanyoyin da za su kawo ci gaba a kungiyar.

Taron dai shi ne na farko da aka yi shi wanda ya samu Halartar mutane masu yawa, wanda Hakan ya nuna masu harkar fim din sun amince da sabon jagorancin na Ado Ahmad Gidan Dabino MON, musamman dai ganin sa a matsayin tsohuwar zuma a cikin masana’antar Kannywwod tun lokacin samar da ita.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *