September 18, 2026

Ƙoƙarin Hon. Usman Nadada Akan Samarda Sabon Birni Da Ma’aikatar Ƙasa Da Sufiyo Ta Jihar Katsina Zata yi

0

Daga Alƙalamin Yakubu Lawal

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya bai yi shinge ko iyaka akan cewar sai wanda ya kware a Ma’aikata ko sashe ake nadawa ba mukami a matsayin Mamba na majalisar zartaswa a matakin jiha ko Tarayya.

Sai dai idan aka yi gamo-da-katar abin ya fi haifar da mai ido idan aka baiwa mutuminda ya fi kwarewa a Ma’aikata ko sashe da aka nada shi ya Jagoranta.

Ma’aikatar Kasa da Sufiyo ta Jahar Katsina, na daga cikin wuraren da suka dace da kwararren Jami’in Tsara Birane(Town Planner) da ke shugabantar Ma’aikatar, wato TPL. Usman Nadada.

Wannan dama da Tpl.Usman Nadada ya samu bayan shekarun da ya dauka yana aiki mai alaka da tsara birane tun bayan kammala karatunsa na digiri na daya da na biyu, wanda har ya kai shi ga rike kujerar Janar Manajan Hukumar Tsara Birane da yankuna na jihar har Katsina na tsawon shekaru ya sanya yake da ra’ayi na ganin cigaban harkokin da suka jibanci Kasa da Sufiyo.

Kudurori da Manufofin da TPL Usman Nadada ya hau mukamin kwamishinan Ma’aikatar da su na tunanin dorawa daga inda wanda ya gada ya tsaya a kan inganta tsarin Kasa sune sirrin nasarorin da ya ke cigaba da samu a Shugabantar Ma’aikatar.

Wannan tsari kuwa shi ne, sarrafa Kasa kai tsaye a maimakon rarrabawa ba tare da sarrafawa ba.

A karkashin wannan tsari ne aka yi tunanin samarda wani sabon birni da zai kunshi kayan more rayuwa dabam-daban da mutanen da za a haifa a sabuwar duniyar za su amfana da su.

Wannan sabon birni da za a kafa a Arewacin garin Katsina, a kan hanyar Katsina zuwa Jibia an rada masa suna’KATSINA RACE COURSE VILLAGE’

Idan wannan birni ya kammalu zai kunshi Gidaje, Makarantu,Massallatai gami da Filayen Wasanni dabam-daban, musamman na Wasannin tseren Dawaki da na Kwallon Dawaki.

Shedar yiwuwar wannan aiki tuni Ma’aikatar Kasa ta yi yarjejeniya da wani kamfanin tuntuba na wasu kwararrun masu ilmin tsara birane mai suna ‘BIN-HAJJ CONSULT’ da ya samarda taswira ta zahiri da bayyana kwarangal din birnin baki daya.

Tuni wannan taswira ta samu sambarka da amincewar Maigirma Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Maimarbata Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da sauran masu ruwa da tsaki.

Wani abun da ya kamata mutane su sani shi ne tuni an fara rattabawa takardun yarjejeniyoyi hannu da kamfanonin da ke huldar samar da muhalli(Developers) don cigaba da tabbatuwar samuwar wannan sabon birni.

Irin wannan shirye-shirye wadanda duniyar cigaba suka yi nisa ga aiwatar da su,a kasashe irin namu na ifrikiyya ba a cika samun aiwatar da su dari bisa dari ba.

Don haka, kaifin basira da hikima ta Kwamishinan Kasa da Sufiyo a Jahar Katsina Tpl.Usman Nadada ya yi amfani da kwarewar da ya ke da ita ta wannan fuska ya hannanta kula da tafiyar ga Kamfanin BIN-HAJJ CONSULT don haka ta cimma ruwa.

Wani sabon salo da Tpl. Usman Nadada ya yi wa wannan aiki tare da shawarar abokan aikinsa da kuma amincewar gwamnati shi ne wannan birni shi zai samarda kansa da kansa.

Yanzu nan da wasu ‘yan lokutta da yardar mai duka sabon birni zai wanzu a nan Katsina,sai dai sanin karkashin wace gunduma zai kasance, muna jiran masana tsare-tsaren iyakoki su bayyanas.

Ko ba komai, ajiye kwarya a bisa gurbinta ta kara tabbata a Ma’aikatar Kasa da Sufiyo ta Jahar Katsina

Alkalamin: Yakubu Lawal
Dan Jarida
Jami’in Hulda da Jama’a.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *