Kitimurmurar Da Ke Faruwa a Hukumar Tace Finafinai ta Kano.
Daga TY Shaban
AN kafa Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano ne sakamakon ƙoƙari da hoɓɓasan da su masu sana’ar shirya finafinai su ka yi na tsaftace sana’ar su da kan su a lokacin gwamnatin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a zangon sa na farko.
An kafa hukumar ne domin ɗaga darajar sana’ar da tsaftace al’amuran finafinai domin su yi daidai da al’adun mu, zamantakewar mu da addinin mu.
Bayan wani lokaci, hukumar ta faɗaɗa komar ta wurin faɗaɗa ayyukan ta zuwa wasu al’amuran kamar kula da bibiyar rajistar gidajen kallo, masu tallar magunguna, ɗab’i da mamaye harkokin tafiyar da ƙungiyoyin masu shirya finafinai kamar rajista ta ‘ya’yan ƙungiyoyi da ma wasu abubuwan.
Hakan ba ya cikin hurumin kundin tafiyar da hukumar na shekarar 2001/2002 kuma babu wani gyara da gwamnati ta yi a hukumance har ya zuwa yanzu.
Ba a nan Gizo ke saƙar ba. Duk da irin tsangwama da tursasawa da hukumar ke yi wa jarumai, furodusoshi, daraktoci da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fim, ‘yan Kannywood na ƙoƙarin yin biyayya ga duk al’amuran hukumar saboda a zauna lafiya duk da sanin cewa akwai wurare da dama da ake hawan ƙawara wurin tafiyar da hukumar.
Bayan wani nazari na bincike da mu ka yi, mun gano wasu abubuwan da ke faruwa waɗanda su na da buƙatar kawo ɗauki da gyarawa domin cimma nasarar hukumar da kyautatuwar masu sana’ar fim, kamar haka:
1- Akwai tsarin rajista da sabunta ta da hukumar ta bijiro da shi, wanda a kan yi a duk shekara, kuma hukumar ta na ɗaukar tsattsauran mataki tun daga watan farko na Janairu ba tare da ta yi duba da durƙushewar tattalin arziki da masana’antar ke fuskanta ba, ƙalubalen rashin aikin yi.
Babu ɗaga ƙafa a watanni uku na farkon shekara, kuma babu tuntuɓa ko bin wata hanya da za a sanar da masu sana’ar cewa lokaci ya yi da ya kamata a zo a sabunta rajista kamar yadda sauran hukumomin tattara haraji su ke yi, sai kawai idan mai shirya fim ya zo neman takardar izinin ɗaukar fim (permit) – wanda shi kan sa wannan ɗin ba bisa ƙa’ida ya ke ba – sai a tursasa shi a kan sai ya biya kuɗin sabunta rajista na kowane ɗan wasa da ya zaɓa zai saka a cikin fim ɗin sa.
Wannan ba daidai ba ne. Ba ma haƙƙin furodusa ba ne biyan kuɗin sabunta rajistar ɗan wasa.
Ga kuma bada lasisin da hukumar ta ke yi ga duk wani wanda ya zo neman wani abu ba tare da wata takarda daga hannun ƙungiyoyin finafinai ba domin sahalewa.
mujallar Fim
