September 18, 2026

Wuya Makarantar Kare: Ba Zan Shiga Yaki Da Kasar Rasha Ba -Shugaban Kasar Amurka

0

Shugaban na kasar Amurka Joe Biden wanda ya gabatar da jawabi a zaman hadin gwiwa na shekara-shekara da majalisun dokoki da dattawa ke yi, ya ce; Babu yadda za a yi kasarsa ta shiga cikin yaki da kasar Rasha,amma dai za ta yi kokarin hana Rasha yin kutse cikin wasu kasashen na turai.

Shugaban kasar ta Amurka ya kara da cewa; Amurka za ta kare kowane taku na kasashen da suke mambobi a kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.

Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce; Amurka da kawayenta sun kakabawa Rasha takunkumi mai tsanani da zai hana ta samun kere-kere na zamani.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *