September 17, 2026

Kungiyar 13 X 13 Ta Fitar Da Fursononi 33 Tare Da Basu Jari A Jihar Sokoto.

0

Daga El-Zaharadeen Umar

Kungiyar 13X13 mai rajin taimakawa marasa karfi ta sake bulla a wani sabon yunkurinta domin tallafawa masu karamin karfi a jihar Sakwato inda ta yi sanadiyar mutune 33 da suka shaki iskar ‘yanci daga gidan gyaran hali na jiha Sakkwato.

Kamar yadda El-Mu’azu Birniwa daya daga cikin ‘yan kwamitin, ya fara bayanin cewa sun zo garin Sakowato ne domin ganin wannan kungiya ta 13X13 ta fitar da mutanen da bashi ko wata tara ta dabaibaye su ta hanasu sakat a wannan gida na gyaran hali.

Haka kuma ya kara da cewa hakan na faruwa ne a dalili kudirorin ita wannan kungiya ta 13X13 wanda daya daga cikin manufofinta shi ne ganin an taimaki wanda baya da shi, ba tare da nuna banbanci ba, kuma babu siyasa a cikin wannan tafiya kamar kowa ya sani.

Tawagar kungiyar 13X13 karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) sun isa sakwato birnin Shehu a gidan gyaran hali na ‘Medium Security Costodian Center’ da ke tsakiyar garin Sakkwato domin gudanar da wannan muhimmin aiki.

Tun da farko an zabi mutane 33 da suke da laifufuka daban-daban da suka hada bashi da kuma wadanda kotu ta yi wa tara amma ba su da halin biya, kuma hakan ne yasa suke zaune a gidan gyaran hali.

Wannan kungiyar 13X13 ta biya dukkanin tarar mutane talatin da uku, sannan kuma aka ba su jari da za su rike a hannu domin fara wata sana’a don dogaro da kansu.

Da yake nasiha ga wadanda suka samu iskar ‘yanci shugaban wannan tafiya Dauda Kahutu Rarara ya fara da yi masu nasihi da cewa kaddara ce ta kawo su wannan gida, saboda haka ya kamata su maida komi na su zuwa ga Allah sannan su rungumi zaman lafiya wanda shi ne Najeriya ke bukata a halin yanzu.

Ya cigaba da cewa, babu dadi mutun ya cigaba da zama wannan gida saboda zaman lafiyar jama’a shi ne zaman lafiya kowa, ya ce duk wanda aka daure ‘yan uwansa suna can basa jin dadi, wani yana da mata, wani kanne gareshi, wani iyaye da dai sauransu.

“Mun fitar da ku ne tsakaninmu da Allah da zuciya daya, Allah yasa kuma ku taimake mu ku rungumi zaman kafiya, duk abinda zamu yi mu tuna cewa Najeriya ce farko, babu maganar siyasa idan ana maganar a zauna lafiya, kuma ina wannan magana ne a madadin kungiyar 13X13, sannan muna son jama’a su yi koyi da abinda muka, kuma wata rana ku yi tunanin ce an fitar da ku, ku fitar da wasu.” Inji shi.

Ita ma da take raba tallafin ga wadanda suka shaki iskar ‘yan ci a madadin kungiyar 13×13, Hajiya Saratu Gidado (DASO) ta fara ne da yi masu nasiha da cewa su din nan masu iyali ne, kuma wata za a yi alfahari da su saboda haka take fatan cewa kadda su sake maimaita irin wannan laifi.

Hajiya Saratu ta ce ko da sayar da kayan miya ne mutun zai iya farawa da dan abinda aka ba shi, sannu a hankali wata rana sai Allah ya albarkacin abin ya zama wani hamshaki, ba yadda Allah bai iya ba.

Daga cikin wadanda suka yi bayani a madadin wannan kungiyar ta13x13 akwai Ibrahim Maishinku da Adam A. Zango da Yakubu Muhammad da Isah Bello Ja da Hajiya Hadiza Muhammad da sauransu.

Suma da suka zamu wannan tagomashin, wasu daga cikin mutane 33 da suka kubuta daga wannan gida sun nuna godiyarsu a madadin saura, inda suka yi alkawarin cewa za su gyara halinsu anan gaba, sannan suka yi godiya ga wannan kungiya ta 13×13 da kuma jagoranta Dauda Kahuta Rarara da wadanda suka rufa masa baya..

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *