Kamfanin DM Kurfi Da KEDCO Sun Kulla Yarjejeniyar Kasuwanci A Katsina
Kamfanin DM Kurfi mallakin Alhaji Danlami Muhammad kurfi sun amshi manya hanyoyin bada wutar lantarki guda biyu daga hannun hukumar wutar lantarki ta KEDCO wa wani huddar kasuwanci tsakaninsu.
Bisa wannan tsarin, kamfanin DM Kurfi ya dauki ma’aikata har mutum tamanin da shidda (86) a karon farko sannan zai kara daukar wasu anan gaba domin Inganta yadda yake gudanar da aikinsa
A yarjejeniyar kamfanin DM kurfi zai rike duk huddar kudi da ya kama a duk layin baban Titin IBB da ya ratsa garin Katsina da kuma bangaran Muhammadu Dikko.
A yau juma’a 12/2/2022 aka kammala mika layukan wutar lantarkin guda biyu da ke kan baban hanyar IBB da kuma bangaran Muhammadu Dikko ga kamfanin DM Kurfi.
Anyi taron a wani dan karamin buki tsakanin sabbin ma’aikatan da kamfanin DM Kurfi da tsaffin ma’aikatan da kuma manajan KEDCO mai kula da shiyyar ta IBB da Muhammadu Dikko.
