Samar Da Kungiyoyin Tsaffin Dalibai Yana Da Mahimmacin Gaske – Dr. Abubakar Munjibir
An bayyana muhimmancin dake akwai wajen samar da ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai domin samun cigaba ga makarantu, da sada zumunci da haɗin kai.
Mai riƙon muƙamin shugabancin ƙungiyar tsofaffin ɗaliban nazarin aikin jarida ta Jami’ar Bayero, Dr. Abubakar Shehu Munjibir, shine ya bayyana hakan a taron manema Labarai da ƙungiyar ta kira a shirye-shiryen gudanar da bikin cikar sashen shekaru 40 da fara yaye ɗalibai a fannin aikin jarida.
Dr. Munjibir yace an shirya taron ne domin haɗa kan ‘ya’yan ƙungiyar tare da bayyana irin cigaban da sashen ke samu.
A karshe yace an shirya lakca ga ɗaliban da ke karatu a yanzu haka, domin sanar da su hanyoyin da za su bi wajen amfani da abinda suka koya don zama masu dogaro da kansu.
