September 17, 2026

Gwamnatin tarayya ta gano wasu dake taimaka ma ƴan ta’adda da kuɗaɗe.

0

Gwamnatin tarayya ta ce binciken da hukumar gano kuɗaɗen da suka saɓa ƙa’ida ta Najeriya ta gudanar ya nuna cewa, mutane 96, da kamfanoni 123, da kuma wuraren ƴan canji kuɗi 33 na taimaka ma ƴan ta’addan Najeriya.

Ministan yaɗa labaran Nigeria Lai Muhammad ya sanar da hakan a Abuja a lokacin gudanar da taron manema labarai, inda ya ƙara da cewa an gano masu taimaka wa masu ba ƴan ta’addan kuɗaɗen guda 424.

Ya ce an kama tare da tsare mutane 45 da ake zargi da yin wannan aiki ne biyo bayan gudanar da binciken, kuma za a gabatar da su a gaban kotu bada jimawa ba.

Kazalika, ministan ya ce an gano wasu ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane da kuma masu haɗa kai a aikata laifi su 25.

Ministan dai na magane ne a wurin taron manema labarai na baje kolin nasarorin da gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta samu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *