September 17, 2026

Gwamnan Jihar Gombe Alh. Muhammadu Inuwa Yahaya Ya Rabawa Wasu Jajirtattun Magoya Bayansa Motoci Da Baburan Hawa Da Kuɗi

0

A Yau Ne Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya (Dan Majen Gombe) Ya Sharewa Wasu Jajirtattun Magoya Bayansa, Inda Ya Basu Motoci Guda Shida Da Baburan Hawa Guda Hudu Da Tsabar Kudi Har Naira Dubu Dari Shida.

Daga Cikin Wadanda Suka Amfana Da Motocin Har Da Alhaji Abubakar Jauro Tela (JT) Da Alhaji Bappayo Tambari Wadanda Suka Sami Mota Samfurin Jeep Kowanensu.

Sai Kuma Alhaji Babayo Kwairon Gwamna Da Adahama Da Wasu Masoyan Gwamna Biyu Suka Samu Mota Samfurin Peugeot 406.

Haka Kuma Yaran Adahama Su Hudu Kowanensu Ya Samu Babur Samfurin Kasea Kowanensu.

Sannan Wasu Yaran Adahama Su Shida Su Kuma An Basu Naira Dubu Dari Kowanensu.

Alhaji Jauro Tela Yayi Jawabi Mai Ratsa Zuciya Game Da Wannan Karamcin Na Mai Girma Gwamnan Jiha Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya.

Yace A Madadin Dukkan Wadanda Suka Amfana Suna Godiya Da Wannan Alheri Na Mai Girma Gwamnan.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *