September 18, 2026

An Kaddamar Da Shirin Aikin Gyaran Ido Kyauta Karkashin Gidauniyar Aminu Bello Masari.

0

Ruhontonni sun tabbatar da cewa gidauniyar Aminu Bello Masari ta kaddamar da shirin fara aikin gyaran ido kyauta ga masu lalurar ido, a shiyyar katsina ta tsakiya.

Jaridar Rana24 ta ruwaito gidauniyar karkashin jagorancin Shugaban kungiyar Alh. Kabir Mashi (kaigaman katsina) ta kaddamar da fara wannan aikin na idon.

Hakazalika dai wannan gidauniya ta Aminu Bello Masari Watau (Aminu Bello Masari Foundation), an assasa tane domin taimakon al’umma musanman marayu da marasa galihu.

Bugu da kari a shekarar data gabata, gidauniyar tayi wani gagarumin aiki, inda ta raba kekunan hawa na guragu kyauta ga masu lalurar, a fadin Jihar katsina. Wanda yawansu yakai sama da guda dari biyu.

Gyaran idon ba a shiyyar ta katsina kadai zai tsaya ba, za a fadada shi zuwa sauran shiyyoyin Jihar Katsina watau shiyyar Daura da shiyyar Funtua.

Wanda maza, mata, Yara, tsofafi zasu amfana da shi

Da yake gabatar da jawabinsa yayin da yake kaddamar da shirin ya bayyana cewa” wannan shirin na gyaran ido yana cikin tsare, tsare Gidauniyar da ta shirya zata rika gudanarwa. Daga karshe ya bayyana yadda tsarin gyaran idon zai kasance.

Ata bakin Shugaban Gidauniyar ya ja hankalin wadanda su ka amfana gyaran dasu kula da bin ka’idar da likitoci su ka basu domin kaucewa samun matsala ga gyaran idon da akayi masu.

Abangaren wadanda su ka amfana da tallafin gyaran idon sun  godema Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari da ya assasa gidauniya domin tallafa ma Marayu da marasa galihu.

Shugaban gidauniyar ya samu rakiyar Sakataren Gidauniyar kuma mai baiwa gwamnan jihar katsina shawara akan harkar tsaro Alh. Ibrahim katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *