September 17, 2026

Baban Jojin Jihar Katsina Ya Rantsar Da Sabbin Alkalan Shari’ar Muslunci A Katsina

0

Alkalin Alkalan jihar Katsina, Mai Shari’a Musa ‘Danladi Abubakar ya rantsar da sabbin alkalan kotun Shari’a guda tara.

Bikin wanda aka gudanar da bikin rantsuwar a baban ɗakin taro na mai shari’a Umar Abdullahi da ke cikin babbar kotun jihar kuma ya samu halartar ‘Yan uwa, abokai da Dangi na wadanda aka nada.

Bikin rantsar da sabbin alkalan kotun Shari’a na daga cikin ayyukan da ke nuna farkon shekarar shari’a ta 2023 a jihar Katsina.

Da yake jawabi a wajen taron, Babban Alkalin, Mai Shari’a Musa ‘Danladi Abubakar ya bayyana rantsuwar a matsayin wani abin tarihi na ci gaban Shari’a a jihar Katsina

Mai shari’a Musa ‘Danladi Abubakar ya yi kira ga sabbin Alkalan kotun Shari’a da su tabbatar da amincewar da babbar kotun jihar ta yi musu na ci gaban al’umma baki daya.

Babban Alkalin ya umarce su da su tsananta neman ilimin addinin Musulunci da kuma kasancewa masu kyawawan halaye don kare martabar bangaren shari’a.

Mai Shari’a Musa ‘Danladi Abubakar ya jaddada bukatar Alkalai su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da aka dora musu na saurin yanke hukunci.

Magatakardan babbar kotun shari’a ta jihar, Barista Nuruddeen El-Ladan Ahmed ya ce an zabi sabbin alkalan kotun Shari’a ne bisa cancanta kuma ya bukace su da su zama jakadu na kwarai na bangaren shari’a a kowane lokaci.

Sabbin Alkalan kotun Shari’a da aka rantsar sun hada da Jamilu Abdullahi Cikin Gida, Nafi’u Rabi’u Usman, Ashafa Abubakar, Hassan Kabir Isma’il, Umar Mukhtar Danjana, Yusuf Lawal Kuirngafa, Anas Bara’u, Lawal Dan-asabe da kabir Al-hassan.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *