September 17, 2026

Zaɓen 2023: Matasan Bade/Jakusko Sun Bayyana Cikakken Goyon Bayan Su Ga Hon. Ahmad Kaitafi

1

Daga Muhammad Aminu, Yobe

Matasan jam’iyyar APC daga ƙananan hukumomin Bade da Jakusko a jihar Yobe, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Hadimin (S.A Protocol) ga Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya- Hon. Sani Ahmed Kaitafi tare da kiran ya gaggauta fitowa takarar kujerar majalisar wakilai don samun ingantaccen wakilci a yankin.

Haka zalika, matasan sun ƙeƙasa ƙasa tare da tsayuwar mashi cewa wannan karon babu wanda za su zaɓa a 2023 face wannan matashi sabon jini, tare da bayyana cewa sun gaji da gafara sa babu ƙaho a mulkin yankin wanda tun bayan ƙirƙiro jihar wani matashi bai taɓa shiga hannun sabbin jini ba.

Sun ce kan mage ya waye, sun kala an daɗe ana ruwa ƙasa na shanye wa- abin da suka bayyana kura da shan bugu gardi da karɓar kuɗi.

A wani gangamin da matasan suka gudanar a Damaturu, fadar jihar Yobe, matasan sun ayyana matashin a matsayin mai halin dattawa, girmama jama’a tare da ƙoƙarin inganta rayuwar al’umma, kana jajjirtacen da baya nuna bambancin yare a ayyukan sa na alheri ga jama’a, musamman a ƙananan hukumomin Bade da Jakusko a jihar Yobe.

Haka kuma mutum ne da ya samu kyakkyawar shaida kuma wanda ya dace ya wakilce yankin a zauren majalisar wakilai a zaɓen 2023 mai zuwa.

Bugu da ƙari kuma, sun shaidar da cewa Hon. Sani Ahmed Kaitafi shi ne matashin da ya dace ya wakilci yankin saboda cancantarsa, saboda yadda ya fahimci matsalolin da al’ummar yankin ke fuskanta, sannan da jajircewarsa a fanin nuna bajinta da kyakkyawar mu’amalar da ke tsakanin shi da jama’a, faɗi-tashin tallafa wa jama’a, kana uwa-uba, kishin da yake nuna wa yankin, al’amarin da ya bambanta shi da sauran yan siyasa da masu rike da mulki a yankin.

Har wala yau, al’ummar sun lashi takobin bai wa maras ɗa kunya wajen ganin haƙarsu ta cimma ruwa, tare da nanata cewa, wannan karon ba za su ƙara maimaita kuskuren da suka tabka a baya ba, wajen yin zaɓen da basu gamsu dashi ba. Sun bayyana cewa, “A wannan karon, In Sha Allah a zaɓen 2023, za mu zaɓi cancanta ne kawai, kuma mun dena yarda da zaɓen tumun dare; sai mutumin da ya dace, wanda ya san qima da martabar wannan yanki ne kawai zamu zaɓa- kuma a halin yanzu shi ne Hon. Sani Ahmed Kaitafi.”

“Haka zalika kuma, idan dai jama’a ke zave kuma jam’iyyar ta na tsayar da ɗan takara bisa ga ra’ayin jama’a; to muna kira ga shugabannin jam’iyyar APC a jihar Yobe, musamman Maigirma Gwamna Mai Mala Buni, shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe- Alhaji Muhammad Gadaka da sauran manyan jiga-jigan APC da masu faɗa aji, muna roƙon su da cewa ‘mu al’ummar Bade/Jakusko, mun amince da Hon. Sani Ahmed Kaitafi a matsayin shi ne xan takararmu a zaɓen 2023 mai zuwa. Kar su ce bamu sanar dasu ba.”

Muhammad Alhaji Adamu (Zarami) Gashu’a ya na ɗaya daga cikin masu wannan furucin, kuma ya ƙara da cewa, “kowa ya san Ahmad Kaitafi mutum ne mai biyayya ga na gaba dashi, kuma mai mutunta duk wanda ya zauna dashi, wannan sanannen abu ne ga duk xan da aka haifa a Bade ko Jakusko. Sannan ɗaukaka da ƙimar da ya samu ta na da alaƙa da biyayyar da Hon. Kaitafi yake da ita. Saboda Malamai sun gaya mana cewa, abubuwan uku su na kai mutum ya samu ɗaukaka a rayuwa, su ne; biyayya, taimako da kyautata wa jama’a. Saboda haka Ahmed Kaitafi ginin Allah ne, duk da wasu na yi masa kallon matashi, amma kuma mai halin dattaku wanda ba ya sauraron gulma ko ƙananan maganganu.”

Ya ƙara da cewa, kasancewar Hon. Kaitafi matashi shi ne ya dace ya wakilci al’ummar Bade/Jakusko a zauren majalisar wakilai a 2023, wanda kuma yin hakan tagomashi ne ga yankin, saboda yadda jama’a suka nuna gamsuwar su tare da amince masa, sannan wannan ya na da alaƙa da kyakkyawar shaidar da kowa ya yi masa, saboda bai tava nuna gajiyawa ko ƙosawa da abubuwan da yake wa jama’a.

“A matsayin mu na matasa kuma ‘yan siyasa, mun yi la’akari da hazaƙarsa, dattakun shi da taimakon da yake yi wa jama’a a kowane fannin ci gaban rayuwa, musamman ilimi wanda yanzu haka ya ɗauki nauyin karatun marayu bila-adadin, kuma ba tare da nuna bambancin addini ko yare ba, kuma irin waɗannan tallafin sun taimaka wajen rage halin ƙuncin da matsalar tsaro ya jefa matasanmu a jihar Yobe.”

Muhammed Alhaji Adamu ya ƙara da cewa, “Saboda haka mu na roƙon Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya dubi girman Allah da Manzonsa (SAW) ya daure ya fito ya yi wakilci al’ummar Bade/Jakusko a zaɓen 2023 mai zuwa.

Sannan kuma muna kira ga Maigirma Gwamna Mai Mala Buni, shugabannin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki a siyasar Arewacin Yobe, musamman a ƙananan hukumomin Bade/Jakusko cewa wannan shi ne zaɓimu a matsayin matasa.”

Ya ƙara da cewa, “Wannan kira ne na baki ɗayan matasan da suka yarda damu a siyasance, kuma mun ɗauki wannan matakin ne biyo bayan tuntuvar da muka gudanar a kowane ɓangaren al’ummar Bade/ Jakusko, wanda yanzu muka ga lokaci ya yi wanda za mu fito fili mu bayyana wa duniya matsayarmu tare da ayyana cewa a shirye muke wajen ganin haƙarmu ta cimma ruwa ta hanyoyin da suka dace wajen bai wa Sani Ahmed Kaitafi cikakken goyon baya, ganin cewa duniya ta ci gaba ta hanyar shelanta ra’ayin ka ta kafafen yaxa labaru na jarida da kafar sadarwar zamani, sannan da kasancewar ɗan takararmu nagari ne wanda kowa ya san alherin sa da mutuncinsa kuma karɓaɓɓe ne ga kowa, kuma Allah zai taimake mu kan wannan kyakkyawar manufa tamu.”

Ya ce, “Saboda gaskiyar magana a baya an sha mu mun warke, wanda a wannan karon kan mage ya waye, babu wanda zai yi wa matasanmu barazana; bamu da shakkar tunkarar duk wanda zai kawo mana cikas, saboda tafiyar ta matasa ce waɗanda su ka shirya kan dukan ƙalubalen da zai tunkare sun dena ci da guminmu.”

A ƙarshe ya ce, “Sannan ina yi wa al’ummar Bade/Jakusko kyakkyawan albishir, kan cewa Hon. Sani Kaitafi ya na da wasu muhimman shirye-shirye wajen aiwatar da tallafa wa matasa da sauran al’ummar wannan yankin- amma ku kasa kunnuwa, ba zan furta ba sai abin ya faru in sha Allah.” Ta bakin shi.

A nashi ɓangaren kuma, Mallam Auwal Ɗan-Chairman ya bayyana wasu daga cikin muhimman ayyukan raya waxannan yankuna, waɗanda Hadimin shugaban Majalisar Dattawan ya gudanar don tallafa wa jama’a: a fannin tallafin karatu, na bunƙasa kiwon lafiya, bai wa matasa kuɗaɗen fara ƙananan sana’o’i da makamantan su.

“Saboda an ɗauki lokaci wanda duk lokacin da muka samu ƙorafi ko neman taimako ga majinyata, musamman na gaggawa, da zaran an faxa masa nan take zai tallafa da kuɗin aljihun shi. Sannan kowace shekara yana ɗaukar nauyin feshin magunan yaƙi da sauro tare da bayar da magungunan zazzaɓin cizon sauro a Asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya don taimako ga jama’a.”

Mallam Auwal ya ƙara da cewa, kowace shekara Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya na biya wa ɗaruruwan ɗalibai tallafin karatu a matakai daban-daban, ciki har da masu rubuta jarabawar kammala sakandire ta WAEC, NECO haɗi da na share fagen shiga jami’o’i JAMB. Baya ga raba littafai da sauran kayan karatu ga ɗalibai, kana da tallafa wa noman wannan yanki da yake bai wa manoma don bunƙasa qasa da abinci- ta hanyar basu takin zamani da kayan aikin lambu.

“Hon. Kaitafi ya taimaka wa matan karkara sama da 200 a wannan yanki da tallafin jarin ƙananan sana’o’i wanda zasu dogara da kansu. Tare da ɗaruruwan matasan da suka samu makamancin wannan tallafi, motocin hawa da na haya, Keke NAPEP

, mashina masu taya biyu kyauta ga matasa don inganta rayuwar jama’a. Sannan da shirya wasannin ƙwallo na sada zumunci tsakanin matasa tare da basu kyautuka don samun ƙarfin gwiwa.”

Ya ce bisa ga wannan da makamantan su, su ne suka jawo hankulan jama’a, mata da matasa suka karkata zuwa ga Hon. Sani Ahmed Kaitafi tare da kira gare shi ya fito takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a ƙananan hukumomin Bade da Jakusko.

Ya ce, “Sannan kuma wannan abu ne sananne ga kowa, wanda babu wata rufa-rufa dangane da bayyana ra’ayin jama’a zuwa gare shi. Kuma babu wanda ya tilasta mana, cancanta da halin dattaku, kyautata wa ga kowa su ne suka jawo muka yanke shawarar bashi cikakken goyon baya.” Ya nanata.

Ita ma Malama Fatima Ibrahim Dachia ba a barta a baya ba, inda ta tofa albarkacin bakinta da cewa, “Alhamdulillah, a matsayin mu na mata ba zamu bari a barmu a baya ba dangane da alharan da Sani Ahmed Kaitafi ya yi mana ba, wanda bisa ga haƙiƙanin gaskiya bamu da xan siyasa matashi da ya kula damu kamar shi. Kuma har ga Allah bamu da abin da za mu bayyana dangane da kyautatawar da yake mana sai addu’a Allah ya saka masa da mafificin alhairi.

Haka kuma sanin duk wani xan wannan yanki ne cewa Hon. Kaitafi hantsi ne; leƙa gidan kowa. Kuma babu wanda ya isa ya zayyana iya tallafin da ya yi mana, sai Allah.”

About The Author

1 thought on “Zaɓen 2023: Matasan Bade/Jakusko Sun Bayyana Cikakken Goyon Bayan Su Ga Hon. Ahmad Kaitafi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *