September 17, 2026

Cutar Kyanda Ta Kashe Mutane 685 A Kasar Zimbabwe.

0

Ma’aikatar kula da lafiyar kasar ta ce wurin karo 4 kenan cutar na barkewa a kasar duk da rigakafin da ake gudanarwa a fadin kasar.

Ma’aikatar ta ce, tana da mutane fiye da dubu 6 da aka tabbatar da sun kamu da cutar, da suka ƙunshi adadin wadanda suka mutun, inji majiyar Popular News Hausa ta FRCN.

Wani labari da ma’aikatar ta ɗora kan shafin ta na Twitter, ya ce an samu karin mutane 191 sabbin kamuwa da cutar, tare da wanda suka mutu su 37 a cikin rana ɗaya, wato ranar 1 ga watan Satumba.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarin Reuters ya bayyana, ministan yada labaran kasar Monica Mutsvangwa ya ce a watan da ya gabata cutar ta fi kama yaran da basu wuce watanni 6 zuwa shekaru 15 da haihuwa ba, masamman wanda addinin su ya hana su amsar rigakafin cutar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *