September 17, 2026

Jihar Nasarawa Ta Samu Masu Cutar kyandar biri 6.

0

An samu mutane shida da aka tabbatar sun kamu da cutar kyandar biri a kananan hukumomi biyu na jihar Nasarawa dake arewa maso tsakiyar Najeriya.

Kwamishinan lafiya na jihar Nasarawa Ahmed Yahaya Baba ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a garin Lafia babban birnin jihar.

Yahaya ya ce mutane shida da aka tabbatar sun kamu da cutar an samu mutum 4 a Lafiya da 2 a karamar hukumar Keffi.

Ya ce gwamnatin jihar ta bude cibiyar kula da cutar ta gaggawa, inji majiyar Popular News Hausa ta AIT.

Kwamishinan ya kuma yi nuni da cewa wadanda abin ya shafa suna karbar magani a Asibitin kwararru dake Lafiya da kuma Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Keffi.

Yahaya ya lissafo wasu daga cikin hanyoyin da ake iya kamuwa da cutar da suka hada da ma’amala da masu ɗauke da cutar kaitsaye da kuma ta shakar numfashi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *