September 17, 2026

Hukumar KASROTA Ta Nemi Goyan Bayan Hukumar Customs A Katsina.

0

Hukumar kula da hanyoyi ta jihar Katsina wato KASROTA ta nemi goyan bayan hukumar Customs wajen sauke nauyin da aka dora mata.

Shugaban hukumar Danlami Yar’adua ya yi wannan rokon a lokacin da ya kai ziyara ofishin konturolan hukumar Customs na jihar Katsina Dalha Wada Chedi.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar Marwana Abubakar ya sanya ma hannu.

Ya ce ziyarar na cikin kokarin hukumar na yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a bangaren amfani da hanyoyi.

Shugaban hukumar ya ce hukumar a shirye ta ke wujen yin jadin gwiwa da masu ruwa da tsaki da abun ya shafa a ƙoƙarinta na tabbatar da ganin an dabbaka da kuma bin dokokin hanya.

Da konturolan Wada Chedi ke maida jawabi, ya yaba ma shugaban hukumar kula da hanyoyin hadi da yan tawagarshi, tare da bada tabbacin yin hadin gwiwa da hukumar a kowane lokaci.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *