An Gudanar Da Taron Wuni Ɗaya Don Magance Cutar Amai Da Gudawa A Katsina
An gudanar da wani taron wayar da kan kwana 1 akan koyar da muhimman hanyoyin magance barkewar cutar amai da gudawa watau cholera a shiyyar Funtua.
Hukumar kula da lafiya daga matakin farko ta jihar Katsina ce ta shirya taron ga malaman kiwon lafiya da jami’an kula da mahalli.
Taron wayar da kan nada nufin sabunta ilimin mahalartan shi akan yadda za su kula da cutar cholera.
Shugaban taron Nuhu Dambo ya bayyana jin dadi ga hukumomi duba da yadda suke kokari wurin inganta ayyukan jami’an kula da mahalli.
Shugaban taron wanda kuma shi ne daraktan sashen samar da ruwa da tsaftar mahalli, ya ce wajibi ne mutane su maida hankali wurin kula da tsaftar mahalli don amfanin lafiyar su.
Abubuwan da suka gudana a wurin taron sun hada gabatar da kasidu.
