September 17, 2026

Haɗarin Tankar Mai Ya Kashe Mutane 2, Ya Raunata 3, Ya Lalata Ababen Hawa 12 a Ogun.

0

Wasu mutane biyu sun kone kurmus, uku sun jikkata, yayin da wasu motoci 12 kuma suka lalace sakamakon haɗarin tankar tankar mai a unguwar Ilo Awela da ke kofar Sango Toll a kan hanyar Lagos zuwa Abeokuta a wannan Alhamis din.

Mrs. Florence Okpe, jami’ar ilimantar da jama’a ta hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC a Ogun ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta.

Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard ta ce, “Hukumar FRSC ta gudanar da aikin ceto a wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 1:30 AM.”

“An shaida wa hukumar kashe gobara, kuma nan take suka isa wurin domin kashe wutar da ta kama”.

“Lokacin da karfe 4:05AM ta yi, motoci 12 sun ci wuta da suka hada da manyan motocin lanziriyos 3, NAPEP 4, babura uku, wata mota daya da kuma tankar mai daya”.

“An ceci mutane ukku tare da kai su asibitin Ota; maza 2 da kuma mace daya da ta kone sosai”.

“An kwashe gawarwaki biyu da suka kone ba za a iya gane su ba daga wurin,” in ji ta.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *