A jiya Litinin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ɗan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya ya jagoranci buɗe ofishin yakin neman zaɓe a kakar zaɓe mai zuwa wanda wasu matasa masu kishi suka samar a madadinsa.
Buɗe wannan ofishi yasa da yawa mutane na ganin lallai Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya fara wannan hidima da kafar dama, domin dai jama’a na tare da shi, kuma sun shirya wajan sake bashi dama ya wakilci wannan karamar hukuma ta Katsina a karo na biyu.
Haka kuma ganin yadda dandazon jama’ar da suka halarci wajan wannan taro da za a iya kiransa na tarihi ya ƙara taba tabbacin nasarar sa a zaɓe mai zuwa idan mai duka ya amince.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya taɓa riƙe wannan kujera da yake neman al’ummar ƙaramar hukumar Katsina su sake bashi dama domin ya wakilce su a majalisar tarayya karo na biyu domin cigaba da samar da ayyukan raya ƙasa da matasa.
Haka kuma shine tsohon kwamishinan matasa jin daɗi da walwalar jama’a na jihar Katsina da ake ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi a rayuwar matasa da kuma harkokin wassani.
Da yake nashi jawabin shugaban matasan unguwar Abbatuwa da Jan Bango da ke cikin birnin Katsina Abdullahi Alkasim ya ce ayyukan cigaba da ya samarwa matasa yasa suka yi tunanin samar da wannan ofishi a madadinsa.
Ya kuma ƙara da cewa zasu tashi tsaye wajan ganin sun tabbatar da nasarar Dan su, wato Hon. Ɗanlami da sauran ‘yan takara na jam’iyyar APC, a zaɓen shekarar 2023 da ke tafe.
Tunda farko shugaban ya bayyana cewa maƙasudin buɗe wannan ofishi shin domin a samar da wani yanayi da zai bada damar a riƙa haduwa da Hon. Sani Aliyu Ɗanlami domin tattauna batutuwan da suka shafi siyasa da kuma jami’yyar APC.
Sai dai a nasa ta’alikin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya godewa matasan su ka buɗe wannan ofishi domin yakin neman zaɓensa wanda suka ya ce sun yi abin a yaba, kuma zai maida biki idan Allah ya bashi nasara.
“Kodayake ba sai na faɗa ba, Abbatuwa unguwa ta ce, mun yi abubuwan alheri da yawa, kuma zamu cigaba da insha’Allahu, shi da muke fata shi ne goyon baya domin a tabbatar da nasarar jami’yyar APC a kowane mataki” inji shi.
Daga karshe Hon. Sani Ɗanlami ya roki alfarmar al’ummar Abbatuwa da Jan Bango da su zaɓi jam’iyyar APC a zaɓen 2023, mai zuwa tun daga sama har ƙasa, domin ci gaba da samar masu da ayyukan raya ƙasa.
