A jiya ne babbar kotun daukaka kara ta Abuja ta bukaci gwamnatin tarayya da mambobin kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da ke yajin aiki da su ci gaba da duba yadda za a warware takaddamar da ke tsakaninsu a wajen kotu.
Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard ta ce, Saboda haka kotun ta dage sauraron karar da kungiyar ta ASUU ta shigar gabanta na tsawon sa’o’i 24.
Ta ce an yanke shawarar ne don ba wa bangarorin da ke rikici da juna damar sake tunani, tare da zama teburin shawarwari, da nufin warware dukkan matsalolin da ke damun su cikin ruwan sanyi.
Mai shari’a Georgewill Biobele Abraham ya bukaci lauyan gwamnatin tarayya Mr. James Igwe, SAN, da lauyan kungiyar ASUU, Mr. Femi Falana, SAN, da su dauki matakin kishin kasa, tare da sanar da shawarar kotun ga bangarorin da suke karewa.
“Akwai lokacin yin komai. A matsayinku na manyan lauyoyi muna son ku nemi hanyoyin sasanta wannan badakalar.”
“Muna sa ran ganin an dawo kotun ranar Alhamis da labari mai daɗi na cewa an sasanta rikicin da ke tsakanin bangarorin 2.”
