Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya a wannan Juma’ar ta tabbatar da mutuwar Duruocha Osita Joel, ma’aikacinta da ya bace a jihar Anambra.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an gano gawar Duruocha a kan hanyar Isu-Aniocha-Urum a karamar hukumar Awka ta Arewa a jihar Anambra, inda wasu da ba a san ko su waye ba suka jefar da shi.
An tabbatar da mutuwarsa a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye.
Sanarwar ta ce, “ma’aikacin INEC, Duruocha Osita Joel, ya rasu a ranar Laraba, 28 ga Satumba, 2022, kamar yadda sakataren gudanarwar hukumar a Jihar Anambra, Okwuonu Jude, ya ba da rahoton bacewar ma’aikacin Duruocha Osita Joel, babban jami’in gudanarwa na hukumar mai mataki na 10.
“A ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba ne, sakataren mulkin hukumar ya kara sanar da cewa, an gano gawar Duruocha a kan hanyar Isu-Aniocha-Urum a karamar hukumar Awka ta Arewa a jihar Anambra, inda wasu da ba a san ko su waye ba suka jefar da shi,” in ji hukumar.
Sanarwar ta ce: “Sauran ma’aikatan hukumar, dan’uwan Duruocha da ‘yan sanda sun dauke gawar tare da ajiye ta a dakin ajiyar gawa.
Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews ta ce, “‘Yan sanda da sauran jami’an tsaro sun fara bincike don gano dalilin bacewar Duruocha da kuma mutuwarsa.”
