Daga Babangida Sunusi, Kano
An bayyana zaman lafiya da kwanciyar hankali na gaba daga cikin burin masarautun gargajiya da su kafi kusanci ga al’umma ne abinda ke gaban iyayen kasa.
Hakan ya fito daga bakin Mai girma Hakimin karamar hukumar Gwale Kuma Dan majen kano watau Alhaji Inuwa Abbas,ya yin wata tattaunawa da wakilin mu a fadar sa.
Dan majen yace ayanzu zaman lafiya shi ne kashin bayan samun walwala ga dukkan wata nau’in Al’umma Kuma abinda ke kawo bunkasar tattalin arzikin kasa da sauran bangarori.
Mai girma Hakimin ya tabbatar da cewa al’umma na bakin kokarin su wajen zabar shugabanni,sai dai shugaban da aka zaba idan yaje matakin da niyyar yi ma wannan jama’ar da suka zabe shi ayukan da alkawalanta ma su,yakan samu batun yasha bambam da abinda yayi tunani.
Bangaren karamar hukumar Gwale kuwa dan maje ya nuna matukar godiya ga jama’ar sa bisa irin biyayya da hadin Kai da suke badawa musamman wajen sa ido da Kuma shelanta matsaloli kafin su zama kalubale dan daukar mataki cikin lokaci.
Sannan ya kuma godema dukkan bangarori na jami’an tsaro da suke da ofishin sa ke aiki da su wajen bada gagarumar gudunmuwa tare da daukar mataki cikin lokacin da ake bukata.
Sai dai Hakimin ya nuna damuwar sa bisa hauhawar farashin kayan masarufi dake damun wannan karni duk da ba wai najeriya bane kadai dukkan duniya ne, Amma dai mutane nacikin yanayin kunci sai dai fatan Allah yakawo saukin abun.
Daga karshe yayi kira ga jama’a da su kasance masu ba dukkan hukumomi da masarautu dama sauran bangarorin tsaro dan samun cigaba da kwanciyar hankali.
