Site icon Popular News

Ƙoƙarin Murkushe ‘Yan Ta’ada: Gwamnatin Katsina Ta Horos Da Ƙarin ‘Yan Banga 600

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

A ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi domin laluɓo hanyoyin murkushe ‘yan ta’ada da ta’adanci da ya addabi jihar shekara da shekaru, yanzu haka dai a iya cewa an kama hanya.

Yaye ‘yan Sintiri da aka fi sani da ‘yan banga alama ce da ke nuni da cewa gwamnatin da gaske ta yi wajan wanin wannan matsala ta tsaro ta kawo karshe a jihar Katsina.

Kamar yadda gwamnati ta yi alƙawari na ɗaukar ‘yan banga 3,000 ya zuwa yanzu ta horas da 110.000 da za su fara tunkarar yan bindiga da suka hana al’umma yin barci da idanu biyu.

Da yake jawabi a wajan taron yaye ‘yan sintiri mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro Ibrahim Muhammad Katsina ya jadadda kudirin gwamnatin Masari na damuwa da sha’anin tsaro inda ya ce wannan sumil taɓi ne ta ɓangaren magance matsalar tsaro.

Alhaji Ibrahim Muhammad, ya yi tuni da cewar a baya ma Gwamna Masari ya ɗauki dawainiyar bayar da irin wannan horo ga ‘yan sintiri kusan 500.

Ya ƙara da cewa yanzu bata sake ba mutum 600 wanda jimla ta kama dubu ɗaya da ɗari ɗaya daga cikin dubu uku da gwamnatin ta yi alkawarin ɗauki tare da ba su horo da kayan aiki da kuma alawus-alawus.

Daga sai mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro ya buƙaci waɗanda aka ba horo da su kasance cikin shirin ko ta kwana sannan su bada haɗin kai ta yadda za su aiki tare da jami’an tsaro daban-daban da suke a yankunan su.

Kazalika shima a nasa jawabin gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Alhaji Muntari Lawal ya bayyana cewa wannan horo da aka yi wa ‘yan sintiri na daga cikin yunkurin gwamnati na kawo karshen ta’adanci a jihar baƙi ɗaya.

Alhaji Muntari Lawal ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ta damu kwarai da halin da tsaro ya shiga a wannan jiha shi yasa ma bata wasa da duk wani abinda ya shafi harkar tsaro bata ɗaukarsa da wasa

Daga karshe ya buƙaci jama’a akan kada su gajiya wurin bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro, domin taimaka masu wurin fuskantar duk wasu masu son zaluntar jama’a.

Anyi wannan kasaitaccen biki ne a harabar kwalejin horaswa ta hukumar civil Defense da ke Babar Riga akan hanyar Batsari da ke cikin Katsina.

A nata taalikin gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina ta bayyana wannan huɓasa a matsayin namijin kokari daga gwamnati sannan ta ce lallai wannan abu yana da kyau abin a yaba ne kwarai da gaske.

A ta bakin shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula Malam Abdulrahaman Abdullahi Dutsima ya ce abinda suke buƙatar gwamnati ta yi shine a tsarewa wadanda suka samu horo haƙƙuƙinsu da kuma kayan aiki, ya ce ta haka kawai wannan shirin zai dore kuma ya samu nasara.

“Kai da gani kasan mutanen nan sun shirya tunkarar ‘yan ta’adda, abinda kawai muke don mu gani an yi shi ne, a tsare haƙƙinsu da kayan aiki da sa ido wajan gudanar da al’amaran yau da kullum” inji shi

Exit mobile version