Site icon Popular News

An Kaddamar Da Gasar Adabin Wakoki Ta Dantakarar Gwamnan APC A Katsina.

Kungiyar Mun Gani A Kasa Ba Labari Ba ce ta kaddamar da gasar akan muhimmin bangarori ukku na adabi ga dantakarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar APC Dr. Dikko Umar Radda mai taken D.U Radda Sabon Shafi.

Da yake jawabi bayan kaddamar da gasar, uban kungiyar ta Mun Gani Gani A Kasa Ba Labari Ba kuma shugaban hukumar kula da gyaran hanyoyi ta jihar Katsina wato KASROMA Injiniya Surajo Yazid Abukur ya yaba ma hangen nesan ƙungiyar bisa bullowa da gasar ta la’akari da cewa mafi yawan mahalarta gasar mata da matasa ne wanda su ne jigon siyasa .

Ya kuma bayyana fatan cewa, gasar za ta taimaka wajen sanya al’ummar jihar Katsina hanyar fahimtar manufar jam’iyyar APC da kuma nagartar dan takarar gwamnan jam’iyyar APC Dr. Dikko Umar Radda.

injiniya Surajo Yazid Abukur ya kara da cewa, yunkurin zai zama wata hanyar share fagen samun nasarar jam’iyyar APC.

Da yake jawabin maraba, mataimakin shugaban jam’iyyar APC Auwalu Bello ya bayyana cewa shirya gasar wanda yake cikin kokarin Injiniya Surajo Yazid Abukur na tabbatar da samun nasarar jam’iyyar APC, tare da karawa da cewa fiddo da gasar na da nufin amfani da fasahohin harshe don inganta tafiya da kuma fiddo da nagartar Dr. Umar Radda.

Kamar dai yadda yace gasar wadda aka shirya don fitar da sakonni masu muhimmancin ga zaben shugaba mai ilimi, wayayye da kuma nagarta, ta kuma ƙunshi bangarorin da suka hada da rubutacciyar waka, rubutun zube da kuma waka.

Auwalu Bello ya kuma ce kungiyar ta na shirya wasannin kwallon kafa don ci gaban matasa, tare da janye masu hankali daga fadawa cikin ayyukan asha.

Haka zalika, yace za a bada kyautar ₦200,000 ga wanda yazo na daya, sai na biyu ya karbi ₦150,000, yayin da na ukku zai samu ₦100,000.

Daga cikin wadanda suka maganta a lokacin bikin sun hada da Malam Jibril Yusuf, Malam Mujahid Abdullahi dukkansu daga jami’ar jihar Kaduna, sai kuma Malam Nagwandu Abukur, da dai sauransu.

Exit mobile version