Site icon Popular News

Hikayata: Labarin Miji Da Matansa Biyu

Wani mutum ya kasance yana auren Mata biyu (2). Maƙota, Ƴan uwa duk sun bada sheda akan yadda yake ƙoƙarin kamanta adalaci a tsakaninsu.

Annoba ta afku, matan biyu suka mutu rana ɗaya kuma lokaci ɗaya.

Saboda ya tabbata ya kamanta adalci a tsakaninsu b tare d nuna fifiko ba, sai y saka aka kirawo masu wankan Gawa mutum biyu domin duk a wanke su a lokaci ɗaya.

Kasancewar gidan Ƙofa ɗaya ce, ya saka aka sake fasa Ƙofa ta biyu domin duk a fiddasu zuwa wajen binnesu lokaci ɗaya.

Haka, duk aka sanya su a cikin Ƙabari lokaci ɗaya.!

Ya dawo gida ya ɗan kishingida yana mai godiya g Sarki Allah da ya ba shi ikon kamanta Adalci. Barci ya kwashe shi saboda gajiya…!

Sai ya yi Mafarki Uwargida tana cewa, ba zan taba yafe maka ba, dama na san kai Azzalumi ne kuma kafi son Amarya…! Cikin mamaki ya ce, menene ya faru haka? Ta ce, in ba don ka tsane ni ba; ta ya ya zaka saka a fidda Amarya t sabuwar Ƙofa, ni kuma a fidda ni ta tsohuwa….!

Exit mobile version