Site icon Popular News

Gwamnatin Najeriya Ta Kaddamar Da Kwamitin Da Za Ya Shirya Bikin Cikar Ta Shekaru 72 Da Samun Ƴancin Kai.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamiti mai mutane 15 da zai yi aiki tsakanin ma’aikatun ta domin tsara yadda za a gudanar da bikin cikar ta shekaru 62 da samun yancin kai.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya kaddamar da kwamitin a Abuja.

A lokacin da yake kaddamar da kwamitin, Boss Mustapha ya ce kwamitin an ɗora mashi nauyin shirya gagarumin taron bikin da zai kawatar.

Ya yi nuni da cewa kwamitin zai saka hukumomi hadi da sauran mutanen da ke da alaka da samun nasarar gudanar da bikin, tare da yin da sauran abubuwan da za su taimaka wurin samun nasarar aiwatar da bikin, inji majiyar Popular News Hausa ta FRCN.

Sakataren gwamnatin ya ce kwamitin zai riƙa zama akai akai don tattauna abubuwan da za a yi a wurin bikin, yayinda kuma za a kafa ƙananan kwamitocin da za su taimaka ma babban kwamitin.

Kwamitin dai zai kasance ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, yayinda babban sakataren kula da harkokin siyasa da tattalin arzukin zai kasance sakataren kwamitin.

Sauran membobin kwamitin sun haɗa da ministan watsa labaran Najeriya, ministan cikin gida, ministar kudi, ministan kula da harkokin wajen Najeriya, ministan Abuja da kuma ministan ayyuka na masamman da harkoki tsakanin gwamnatoci, da dai sauransu.

Exit mobile version