Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya zagon kasa ta saki kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo bayan shafe sa’o’i 48 a hannun ta, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.
Oluomo mai wakiltar mazabar Ifo 1 a majalisar dokokin jihar Ogun, ya koma gidansa dake Ifo a safiyar yau Asabar.
Daruruwan magoya bayansa ne suka tarbe shi da suka hada da shugabannin kungiyar kiristoci a Ifo.
Wani mai taimakawa shugaban majalisar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce kakakin majalisar da jami’an hukumar EFCC suka dauka a filin jirgin sama na Muritala Muhammad da ke Lagos a ranar Alhamis ya dawo gida da safiyar yau Asabar.
Ya ce, “yanzu haka yana gidansa dake Ifo.”
Da aka tambaye shi yaushe aka sallame shi, mataimakin ya ce kakakin ya isa gidansa na Ifo da safiyar yau Asabar .
An kama Oluomo ne bisa zargin aikata laifukan da suka shafi kudi.
