Site icon Popular News

Dalilin Da Yasa Wani Matashi Ya Kashe Kishiyar Mamansa Da Taɓarya. Inji Rundunar ‘Yan Sandan Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cafke Najib Shehu ɗan shekara 25 da ke zaune a unguwar Ambasada a cikin birnin Katsina wanda ake zargi da kashe kishiyar mahaifiyarsa

Kakakin rundunar SP Gambo Isah ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Katsina.

SP Gambo Isah ya ƙara da cewa rashin fahimta ne ya shiga tsakani Najib Shehu da kishiyar Mamansa Malam Asiya Muhammad yar shekara 60 wanda ke zaune a unguwar Ambasada cikin birnin Katsina.

Sanarwar ta cigaba da cewa Najib bai yi wata wata ba ya shiga ɗakin girki inda ya ɗauko tabarya ya cigaba da rusawa kishiyar mahaifiyarsa a kanta, wanda haka yasa ta samu raunuka daga baya likita ya tabbatar da rasuwar ta a asibiti.

“Bayan kwantar da Malama Asiya Muhammad da duka Najib kuma ya farwa mahaifinsa Alhaji Shehu da Duka inda shima ya yi masa karaya a ƙafarsa da kuma wasu wurare a jikinsa” inji sanarwar

Haka kuma kakakin rundunar ya bayyana cewa wanda ake zargin ya shiga hannu kuma ya tabbatar da aikata wannan ɗanyen aiki da ake zargin sa da aikatawa sannan an samu taɓarya a matsayin shaida, haka kuma bincike na cigaba da gudana.

Exit mobile version