Kasar Sin ta harba makami mai linzami da dama a kan mashigar Taiwan, inda suka kai hari a tekun da ke kewaye da Taiwan, bayan ziyarar da shugabar majalisar dokokin kasar Nancy Pelosi ta yi, wadda ta haifar da kazamin fadan soji a yankin gabashin Asiya, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard.
Lamarin da ma’aikatar tsaron Taiwan ta tabbatar da cewa, an harba makami mai linzami kirar Dongfeng na kasar Sin guda 11 a yankin Taiwan tsakanin karfe 1:56 na rana zuwa 4 na yamma.
A halin da ake ciki kuma da yammacin jiya alhamis, sojojin kasar ta Taiwan sun ce suna cikin shirin ko-ta-kwana, tare da sa ido kan ayyukan sojojin kasar Sin a yankin, kuma na’urar radar dake sanya ido mai cin dogon zango a tsibirin ta gano makaman masu linzami dake tahowa.
“Mun yi Allah wadai da irin wannan matakin na rashin hankali da ya kawo cikas ga zaman lafiyar yankin,” in ji ma’aikatar tsaron Taiwan a cikin wata sanarwa.
Biyar daga cikin makamai masu linzamin da aka harba sun sauka a cikin ruwa a kusa da yankin Taiwan wanda ke cikin kebantaccen yankin tattalin arziki da Japan ke kula da shi tare da cewa nata ne, abin ka iya jawo jawo kasar Japan da Amurka shiga cikin lamarin barin wutar.
“Wannan babban batu ne da ya shafi tsaron kasarmu da kuma lafiyar jama’armu,” in ji ministan tsaron Japan Nobuo Kishi, a cewar kafar yaɗa labaran Kyodo News.
A cikin shekaru biyu da suka gabata, kasar Japan ta ci gaba da daukar matakan tabbatar da tsaro, saboda barazanar da kasar Sin ke yi wa Taiwan.
Yasuhide Nakayama, mataimakin ministan tsaron Japan, ya ce “Dole ne mu kare Taiwan, a matsayin kasa mai mulkin dimokuradiyya.”
An dai shirya Pelosi za ta ziyarci kasar Japan ranar Juma’a.
Kasar Sin na ci gaba da gudanar da atisayen soji kai tsaye a yankuna shida dake kewaye da Taiwan. An fara atisayen na hadin gwiwa na teku da na iska da safiyar Alhamis kuma za a ci gaba da gudanar da atisayen a kalla a ranar 7 ga watan Agusta.
Kasar Sin ta ce ta harba jiragen yaki da dama, da jiragen bama-bamai, da jiragen ruwa da kuma jiragen gargadi na farko zuwa tekun dake kewayen Taiwan a safiyar ranar Alhamis. Ma’aikatar tsaron Taiwan ta ce ta gano wasu daga cikin wadannan jiragen, watakila jirage marasa matuka, sun tashi sama da Kinmen na Taiwan, wanda ke da nisan mil kadan daga gabar tekun gabashin kasar Sin, kuma ya yi ta harbin bindiga don korarsu.
Tun a ranar Talata, jiragen yakin kasar Sin suma suke ta shawagi a mashigar tekun Taiwan, wani lokacin ma har kan layin tsakiya dake raba sararin samaniyar kasar Sin da na Taiwan suke zuwa, a cewar rundunar tsaron Taiwan.
