Domin inganta kiwon lafiya ga mata, jarirai da yara, wadda ta kafa gidauniyar Wellbeing Africa, WBFA, Mrs. Toyin Ojora-Saraki ta ce shayar da jarirai nonan uwa ita ce mafi kyawun abinci kuma lafiyayyar bada abinci mai gina jiki ga jarirai.
Ta yi kiran ne a lokacin makon shayarwa na 2022 mai taken, ‘Tsara Shayar Da Nonan Uwa Da Taimakon Ilimi.”
Da yake magana kan mahimmancin shayarwa, Ojora-Saraki, ya ce: “Shayar da nono ita ce hanyar samar da abinci ga jarirai tun farkon rayuwa.
Gidauniyar WBFA a cikin 2018-2021, ta aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki na uwa, kuma ya yi tasiri sosai a wurare 30 da aka zaɓa da kuma al’ummomi 32 a Babban Birnin Tarayya Abuja, jihar Kwara da Lagos, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard.
Ta hanyar shirin, unguwar zome sun nuna ma mata masu juna biyu yadda za shayar da yayansu.
Ta ce shirin ya samar da ci gaba mai dorewa a jihohin da aka ambata sama wajen rage mutuwar jarirai, mace-macen yara, da kuma kamuwa da cututtuka, ta yadda hakan ya inganta alkaluman rayuwa, inda jihar Kwara ke da karancin mace-mace da rashin lafiya a Najeriya.
