Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa reshen jihar Katsina Alhaji Jibrin Ibrahim Zarewa ya bada tabbacin haɗa karfe da karfe da kungiyar ɗariƙa awareness forum, wajan cigaba da wayar da kan jama’a akan abinda ya shafe hukumar zaɓe da zaɓen da kuma rijistar katin zaɓe da ake cikin gudanarwa a fadin Najeriya.
Alhaji Jibrin Ibrahim Zarewa ya bayyana haka a lokacin da shuwagabannin kungiyar ɗariƙa awareness forum Katsina suka kai masa ziyara a shalkwatar hukumar da ke Katsina.
Tunda farko sai da shugaban ya yi wa tawagar ɗariƙa awareness forum cikakken bayani game da ita kanta hukumar zaɓe da kuma irin ayyukan da doka ta sahale mata ta yi akan fannoni daban-daban.
Ya kuma nuna jin daɗinsa da wannan ziyara tare da faɗin cewa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC shirye take ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Ɗariƙa Awareness musamman akan abinda ya shafi wayar da kan jama’a akan batun katin zaɓe da sauran batutuwa a fadin jihar Katsina.
Haka kuma Alhaji Jibrin Ibrahim Zarewa ya ce wannan ziyara an yi ta a lokacin da ya da ce, duk da cewa wuri ya kure amma dai kungiyar na da rawar da zata taka wajan ganin an ƙara samun narasa.
“Wani abu da ba baku sani ba shine, an yi wa jihar Katsina nisa wajan masu yin rijistar katin zaɓe, idan aka duba matsayin jihar Katsina ta huɗu a yawan mutane da masu katin zaɓe, amma yanzu ta koma ta ashirin da huɗu, wanda ba haka muka so ba” inji shi
Kazalika ya yi dogon bayani akan yadda suka samu ƙarin rumfunan zaɓe da wuraren da aka kai su, tare da ɗaukar alƙawarin cewa duk lokacin da hukumar zaɓe zata yi wani taro na masu ruwa da tsaki kungiyar Ɗariƙa Awareness Forum na cikin sahun gaba saboda muhimmanci da irin tsare-tsaren da suke da shi.
Tunda da farko da yake nasa jawabin akan maƙasudin wannan ziyara ta su, shugaban tafiyar kuma ɗaya daga cikin kwamitin amintattu na kungiyar Ferfesa Abdulaziz Ahmad Mashi ya bayyana cewa tuni suka so kawo wannan ziyara amma yanzu Allah baya ƙaddara hakan.
Ya ƙara da cewa suna son haɗa gwiwa da hukumar zaɓe domin bada ta su gudunmawa wajan ganin jama’a sun yanki katin zaɓe kuma kungiyar su bata da alaƙa ta nesa ko ta kusa da kowace irin jam’iyyar siyasa.
Ferfesa Abdulaziz Mashi ya ce bisa haka ne suke neman cikakken bayani game da ayyukan wannan hukuma wanda hakan zai ba su damar sanin ta inda za su bada gudunmawa ganin cewa mafiyawan su a tafiyar matasa ne.
Sannan ya nemi hukumar zaɓe da ta ɗauki kungiyar ɗariƙa awareness forum a matsayin abokiyar tafiyar wajan isar da sako ga al’ummar Musulmi ba wai sai ‘yan ɗariƙa kawai ba.
A nasa ta’aliki sakataren tsare -tsare ba kungiyar, Awwal Abba Yahaya ya bada tarihin kafuwar kungiyar ɗariƙa awareness forum da kuma dalilin da yasa aka kafa ta tare da yin bayanin irin tsarin shugabancin da suke da shi a matakin jiha da shiyya da ƙananan hukumomi zuwa mazaɓu.
Awwal Abba ya ce suna amfani da hanya mafi sauki wajan isar da kowane irin sako ake son isarwa ga mambobin su, ko dai ta hanyar haɗuwa a Masallatai na yau da kullum ko kuma duk sati wajan zikirin juma’a.
“Kimanin shekaru bakwai ke na kafa wannan kungiya wanda take da wakilin kowane ɓangare a ɗariƙa kuma muna da shuwagabanni tun daga matakin jiha da shiyya da kuma ƙananan hukumomin harda matakin rumfa, kuma babu ruwan mu da wata jam’iyyar siyasa, muna yin wanna tafiya ne ganin yadda aka bar mu a baya akan batun siyasa amma yanzu mun farka kuma za a damu da mu” inji shi
Daga karshe sakataran tsare-tsaren ya ce sun shirya tsaf domin cigaba da wayar jama’a akan wannan hidima ta katin zaɓe, inda ya ce za su yi amfani da kafafen yaɗa labarai wajan isar da wannan sakon, tare da bada tabbacin za a ga canji kusa ba nesa ba.
