Site icon Popular News

INEC Zata Rufe Yin Rijistar Katin Zaɓe Ranar 31 Ga Watan Yuli, A Katsina

Daga Mamman Faruƙ, Katsina

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa reshen jihar Katsina ta bayyana cewa a cigaba da yi wa jama’a rijistar katin zaɓe da ake gudanarwa a fadin Najeriya zai zo karshe a ranar 31 fa wannan watan Yuli, 2022

Wannan bayani yana kunshe ne acikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar zaben ta Ƙasa reshen jihar Katsina, Aliyu Garba Adosa ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai a Katsina.

Haka kuma sanarwa ta cigaba da cewa bayan wani taro da masu ruwa da tsaki da hukumar ta gudanar a ranar 15 ga watan Yuli, 2022 inda a karshen taron ta yanke hukuncin cewa a sanar da jama’a za a dakatar da wannan yin rijista.

kazalika hukumar ta bada umarnin ƙara lokacin yin rijistar zuwa karfe 5:00pm na yamma a dukkanin cibiyoyin da ake yin rijistar har da ranakun hutu wato asabar da kuma Lahadi, popular News Hausa ta ruwaito.

Hukumar tace hakan zai ba wanda ya kai shekaru 18 mallakar katin damar zuwa cibiyoyin yin rijista domin samu, tare da ba wasu damar yin gyara da suke buƙatar yin a katitikansu ko kuma canza adireshi wasu daga wata unguwar zuwa wata.

Daga ƙarshe hukumar zaɓe ta ƙasa reshen jihar Katsina ta miƙa godiya ga al’ummar jihar Katsina da ma na ƙasa baƙi ɗaya bisa goyon baya da nuna sha’awar yin katin zaɓe da zai baiwa ɗan ƙasa damar yin zaɓe a Kowane lokaci.

Exit mobile version