Rundunar yan sanda jihar Katsina ta kama wasu mutane biyu data ke zargin fursunonin da suka tsere ne a harin kwanan nan da aka kai a cibiyar gyaran hali ta Kuje dake birnin tarayya Abuja.
Wadanda ake zargin sun hada da Abdulkadir Musa da Kamala Lawal Abubakar.
Bayanin haka na kunshe ne acikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar yan sanda jihar Katsina SP Gambo Isah ya fitar a Katsina.
Sanarwar ta yi nuni cewa an kama daya daga cikin mutanen mai suna Kamala Abubakar a karamar hukumar Danmusa dake cikin jihar Katsina biyo bayan wani samame da aka kai a maboyar yan ta’addan ɗauke da wata tabar wiwi da ake zargin tashi ce.
Yayin da shi kuma Abdulkadir Musa aka kamashi a karamar hukumar Bakori. Ya ce za a mika su ga hukumar cibiyar gyaran hali ta kasa domin daukar matakin da ya dace.
A wani labarin kuma rundunar yan’sandan ta kama wasu yan fashi da makami da suke addabar jihar Katsina da kewayen ta.
Ya bayayana sunayen wadanda ake zargin kamar haka Abdurrazak Isyaku dan shekaru 25, Muhammad Abubakar mai shekara 18, kuma sun kware ne wajen ɓalle gidaje a acikin Katsina da kuma fashi da makami a cikin dare.
Ya kara da cewa rundunar ta kama wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Popular News Hausa.
Ana dai zargin Bello Jino da hada kai da shi wajen garkuwa da mutane da dama acikin garin Katsina, tare da karɓar kudin fansa tsakanin naira dubu 80 zuwa dubu 200 .
Haka zalika rundunar ta kama wasu mutane 6 da ake zargi da kashe malam Dayyabu dake karamar hukumar Kankara a gonar shi, sannan kuma daga bisani suka kai ma matarshi hari a gida da nufin kashe ta, amma ba suyi nasarar samun ta ba, saidai sun lalata wani bangare na gidan.
Bugu da kari rundunar tayi nasarar kama wasu da take zargin yan fashi ne da suka boye gidan wata mata a karamar hukumar Malumfashi.
SP Gambo ya ce dukkan waɗanda ake zargin sun amsa laifin dake ake zarginsu, sannan rundunar za ta gurfanar da su gaban kotun da zarar ta kammala bincike.
