Abokin takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyar APC a babban zaben shekarar 2023 dake tafe ya ce lokaci ya zo da za a kawar da siyasar addini.
Sanata Kashim Shettima ya sanar da hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin membobin jam’iyar APC a wata ziyarar taya murna.
Shettima wanda ya taba yin gwamnan jihar Barno har sau 2, ya bayyana cewa ya kamata yan Najeriya su maida hankali kan yadda za su ciyar da ƙasar su gaba, ba wai a buge ga batun addini ba, inji Popular News Hausa.
Ya ce tuni duniya ta wuce wannan batun, tare da bayyana bukatar ganin an maida hankali ga harkar masana’antu.
Tunda farko, saida tsohon jakadan Najeriya a kasar Amurka Muhammad Hassan wanda shi ne ya jawo tawagar, ya bayyana cewa suna tare da Shattima hadi da sauran tsare tsaren shi.
Ya ce abinda suka maida ma hankali shi ne shirya taron jama’a don bayyana yan takarar ga yan Najeriya.
