Site icon Popular News

Cin Amanar Da Aka Yi Mani Yasa Na Fice Daga APC -Dakta Musa Gafai

Daga Babangida Sunusi, Katsina

Tsohon ɗan takatar majalisar tarayya a ƙaramar hukumar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC kuma matashin Ɗan kasuwa a jihar Katsina Alhaji Musa ya bayyana abinda yake kallo a matsayin cin amanar da uwar jam’iyyar APC ta jihar Katsina tayi masa yasa ya fice daga jam’iyyar bayan da aka bayyana wani a matsayin ɗan takatar kujerar majalisar tarayya a ƙaramar hukumar Katsina.

Fitaccen Ɗan kasuwar wanda ya bautama jam’iyyar APC a ɓangarori daban-daban tare da saɗaukar da dukiyar sa wajen taimakon jam’iyyar a jihar ta Katsina ya bayyana wa wakilinmu haka yayin da ya gana da shi a wata ziyara da wakilinmu ya kaimasa makon jiya.

Gafai ya ɗora wannan zargin ne kachokan kan uwar jam’iyyar ta APC wajen naɗa wani da baici zaɓen fidda gwani ba a lokacin da aka gabatar da zaɓen da aka gudanar a Katsina

Shugaban gidauniyar jin kan al’ummar jihar Katsina watau ‘Gafai Charitable Foundation’ yace lallai a matsayin sa na wanda yake taimakon al’umma ya zama dole ya yi tunanin shiga cikin siyasa dan kara faɗaɗa wannan taimaikon nasa ga jama’a ta wannan kudiri daya bashi damar fitowa siyasa.

Musa ya kuma tabbatar wa wakilinmu cewa lokacin wannan zaɓe an bayyana cewa za’a gudanar zaɓen a local government service commission ta jihar Katsina, amma suka je akace an canza zuwa filin wasa na Muhammad Dikko wanda daga bisani aka ƙara bayyana gurin zaɓe ya zuwa ƙaramar hukumar Batagarawa daga bisani ma ba’a gudanar ba.

Kazalika yace bayan sun yi sallar juma’a a wannan ƙaramar hukumar kasancewar ranar juma’a ne tare da ɗan majalisa mai ci yanzu da kuma Hon Abdurrashid wajen dawowa stadium da akace an maido wannan zaɓe karfe huɗu na yamma suka samu an cika filin wasan na Muhammad Dikko da kauraye da ‘yan banga da wukake da sanduna.

Nan take suka sanar da hukumar tsaro ta ‘yan sanda jihar Katsina dan tsaida wannan zaɓe tare da sama takarda hannu, amma uwar jam’iyyar APC ta jihar Katsina tayi burus da wannan doka tare da baiwa wanda suke zargi da ɓoye deliget nasarar cewa shi yaci zaɓe.

Bayan bayyana wanda suke zargi da ɓoye deliget da kuma kawo ‘yan daba tare da bayyana shi matsayin wanda yaci zaɓe cikin mintuna talatin ne da uwar jam’iyyar APC ta jihar Katsina da ƙaramar hukumar Katsina tayi yake ganin lallai wannan ba jam’iyyar zama bace.

Kuma ba inda yakamata ya cigaba da zama bane da jama’arsa dan rashin adalcin da yake ganin anyi mashi ya bashi damar sauya sheƙa ya zuwa gidan ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar PDP watau Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da ya bayyana bambamcin a bayyane yake.

Exit mobile version