Da safiyar yau Juma’a ne wasu matasa da daliban makarantar Rufus Giwa Polytechnic dake garin Owo, jihar Ondo suka gudanar da zanga-zanga a gaban sakatariyar jihar a Akure, kan kisan da aka yi wa Folarera Ademola dalibin ND1 na sashen nazarin kimiyya da Fasaha, wanda ake zargin wani jami’in Amotekun da yi.
Matasan da suka fusata sun toshe duk wata hanyar dake kewaye da babbar kofar sakatariyar, inda suka hana kai komon mutane da ababen hawa.
Masu zanga-zangar, wadanda suka yi watsi da ruwan sama da aka yi a safiyar yau, sun yi tattaki zuwa gidan gwamnati, tare da kai gawar a wurin, suna masu yin kira ga gwamna Oluwarotimi Akeredolu da ya kamo jami’in Amotekun da ya kashe shi, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership.
Masu zanga-zangar sun kuma bai wa gwamnatin jihar wa’adin sa’o’i 24 da ta mika wannan jami’in ga rundunar ‘yan sandan Najeriya domin gurfanar da shi a gaban kotu, a dauki nauyin binne mamacin, tare da biyan iyalansa diyya.
Da yake magana a madadin daliban, shugaban kungiyar daliban, Olorunda Oluwafemi, ya tabbatar da cewa jami’in Amotekun ne ya harbe dalibin a ranar 26 ga watan Yuni a kofar gidan iyayensa.
Oluwafemi ya kara da cewa marigayin ya ɗauki tsawon kwana 10 yana jinyar harbin bindiga kafin a kai shi asibitin tarayya dake Owo, inda ya ce ga garinku nan ranar Alhamis.
Ya ce daliban da suka yi zanga-zangar sun yi tattaki ne daga kofar makarantar ta fadar Olowo na Owo kafin su yi zanga-zangar zuwa ofishin gwamna da kuma ofishin Amotekun don bayyana takaicin su.
Da take mayar da martani, rundunar Amotekun ta ce tana cikin bacin rai da bakin cikin samun labarin rasuwar wani dalibin makarantar Rufus Giwa Polytechnic, Owo, wanda ake zargin daya daga cikin ‘yan Amotekun ne ya harbe shi a garin Owo yayin da suke gudanar da wani samame.
A cewar kwamandan rundunar Amotekun na jihar, Akogun Adetunji Adeleye, “Dole ne rundunar ta bayyana wa jama’a abin da ya faru a kwanakin baya wanda ya yi sanadin mutuwar dalibin.
“A matakin da ta dauka na tabbatar da cewa jihar Ondo ta kawar da masu aikata laifuka, rundunar Amotekun ta jihar na binciken wani gungun mutane da suka kware wajen kai wa yan achaba farmaki da muggan makamai, tare da kwace musu babura.
Saidai ya ce, ” jami’an Amotekun sun bi ɗaya daga cikin gungun mutanen daya shige cikin wani gini a Owo inda mutanen suka haɗa su 15 a cikin ginin, 7 daga cikinsu suna tsirara a cikin daki da yake cike da hayaƙi. An kuma samu ƴan achaba 4 a cikin dakunan”
“Bayan sun gama gabatar da kan su ga mutanen, sai gungun suka kama kokarin amshe makaman dake hannun jami’an”.
“A kokarin da suke yi na cafke wanda ake zargin, gungn mutanen sun yi kokarin kwace musu makamai, kuma a cikin fafatawar, daya daga cikin bindigogin su ta tashi ta bugi daya daga cikin wadanda ake zargin da kuma wani jami’in Amotekun ɗaya”.
“A lokacin babu daya daga cikinsu ya fadawa jami’an Amotekun cewa su dalibai ne.”
Adeleye ya ci gaba da cewa, a karshe jami’an sa sun yi galaba a kan wadanda ake zargin, inda suka kama su kuma suka kai su ofishin hukumar dake Owo inda aka tsare su yayin da ake ci gaba da bincike.
A cewar sa, lamarin ya faru ne a ranakun 27 da 28 ga watan Yunin 2022.
Kalamansa: “An sake shi ne bisa la’akari da lafiyarsa, inda ya yi alkawarin mayar da shi hannun hukumar domin ci gaba da bincike.
“Wanda ake zargin ya bar wurinmu ne a ranar, kwanaki 11 da faruwar lamarin domin samun kulawar gaggawa tare da alkawarin dawowa a ci gaba da bincike.
“Abin mamaki, mamacin ya mutu ne jiya bayan kwanaki 11 da faruwar lamarin.
“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga ‘yan uwa da abokanan marigayin, yayin da muke ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan ainihin musabbabin mutuwarsa.
“Rundunar Amotekun ta Jihar Ondo, tana so ta tabbatar wa jama’a cewa za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyar dalibai da kungiyar kwalejin kimiyya da fasaha da kuma iyalan wanda abin ya shafa domin ganin an yi adalci.
“Rundunar ta yi alkawarin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kare al’ummar jihar Ondo tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro da kuma tsaftace jihar daga masu aikata laifukan dake ta’addanci a jihar.”
