Site icon Popular News

SWAN A Katsina Ta Gargadi Masoya Kwallon Kafa Dasu Guji Tada Hatsaniya.

Kungiyar marubuta wasanni ta kasa reshen jihar Katsina ta gargadi masoya kwallon kafa dake cikin birnin Katsina dasu guji kawo hatsaniya dama dukkan wani abu daka iya ɓata mutuncin jahar a harkokin wasanni.

Shugaban kungiyar Nasir Sani Gide ya yi wannan gargadin a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar game da wasan karshe na kofin Superleague da ƙungiyoyin Durbi Strikers da Kofar Soro United za su buga.

Kamar yadda sanarwar tace, a lokacin wasan kusa dana kusa da na karshe da kuma wasan kusa dana karshe an samu hatsaniya, inda wasu daga cikin magoya bayan kungiyoyin suka tada hayaniya.

Sanarwar ta roki mahukunta kungiyoyin guda biyu da zasu fafata a wasan karshen dasu jawo hankalin magoya bayan su a lokacin wasan dama bayan wasan.

Shugaban kungiyar wanda ya yabama kokarin hukumar kula da harkokin wasanni ta jihar wajen tabbatar da gudanar da wasannin lami lafiya, ya bukaci hukumar data samar da wadataccen tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma yi amfani da sanarwar wajen yaba ma kungiyar alkalan wasanni ta jihar bisa dakatar da wasu daga cikin qya’yan kungiyar bisa halin rashin dattaka.

Exit mobile version