Site icon Popular News

Majalisar dokokin Kogi Ta Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kogin Ahmed Muhammed ne aka tsige, yayin da kuma wasu manyan jami’an majalisar su uku aka cire su daga mukamansu tare da dakatar da su.

Muhammed shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Akpa 1 a majalisar dokokin jihar.

‘Yan majalisar, wadanda suka yi zaman gaggawa a majalisar dake Lokoja a ranar Juma’a, sun zargi Muhammed da wasu manyan jami’ai uku da aikata muguwar dabi’a da cin zarafin ofis.

A wani kudiri na gaggawa wanda Hon. Enema Paul, mamba mai wakiltar mazabar Dekina/Okura na jihar ya gabatar, ya ce ‘yan majalisa 17 sun rattaba hannu kan batun tsige mataimakin shugaban majalisar tare da dakatar da manyan jami’an majalisar uku.

Kamar yadda jaridar LEADERSHIP ta bayyana, Manyan jami’an uku da aka tsige daga mukaminsu aka kuma dakatar da su daga majalisar sun hada da Bello Hassan Balogun shugaban masu rinjaye, Idris Ndako Mataimakin shugaban masu rinjaye, da Hon. Edoko Moses Ododo babban mai tsawatarwa.

Daga nan ne majalisar ta bayyana Alfa Momoh Rabiu, dan majalisa mai wakiltar Ankpa II a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

Sauran sabbin shugabannin da aka zaba su ne Hon. Muktar Bajeh shugaban masu rinjaye, Umar Isah Tanimu mataimakin shugaban masu rinjaye, Enema Paul mataimakin shugaban masu rinjaye, da Ahmed Dahiru a matsayin babban mai tsawatarwa.

Tun da farko dai, saida shugaban majalisar, Prince Mathew Kolawole, ya sanar da rusa dukkanin kwamitocin majalisar.

Kafin aiwatar da tsigewar dai, an ga ɗunbin jami’an tsaro a harabar majalisar da suka hada da ‘yan sanda, da jami’an tsaro na farin kaya wato Civil Defence, da kuma jami’an tsaron farin kaya wato DSS.

‘Yan majalisar 17 cikin 25 ne suka halarci zaman.

Exit mobile version