A karo na biyu, Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya sake komawa matsayinsa na shugabacin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina.
In dai ba a manta ba, Majigiri ya ajiye shugabancin jam’iyyar ta PDP ne bisa raɗin kansa gab da lokacin kakar gudanar da za6ukan fidda gwanin jam’iyyu a watannin baya, inda ya yanke shawarar shiga neman tikitin takarar kujerar gwamnan jihar Katsina a jam’iyyarsa ta PDP.
Sai dai biyo bayan za6en fidda gwanin na jam’iyyar PDP da ya gudana wanda Allah bai ba shi sa’a a kanta ba, sai yanzu kuma aka sake ba shi jagorancin jam’iyyar ta PDP a matakin jiha.
Tuni dai Hon. Majigiri ya ci gaba da jagorantar sasanta ‘ya’yan jam’iyyar da kuma ɗinke duk wata ɓaraka domin samun nasararsu a zaɓukan 2023 da ake fuskanta.
Babban abin da ke a gaban jam’iyyar ta PDP dai a yanzu shi ne, fitar da wanda zai yi wa Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke mataimaki wanda shi ne aka tsaida a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar a 2023.
